Nelson Chamisa ya kira sakamakon zaben ''mara gaskiya'' Photo: AFP

Madugun 'yan adawar kasar Zimbabwe Nelson Chamisa wanda ya fafata a zaben shugaban kasa ya kalubalanci nasarar da Emmerson Mnangagwa ya yi ikirarin samu.

Mnangagwa, mai shekaru 80 a duniya, ya yi nasara a karo na biyu inda ya samu kashi 52.6 na kuri'un da aka kada, kashi 44 cikin 100 kenan daga adadin da babban abokin hamayyarsa, Chamisa, mai shekaru 45, ya samu a cewar sakamakon da hukumar zabe ta kasar Zimbabwe (ZEC) ta sanar da yammacin ranar Asabar.

Jam'iyyar adawa ta Citizens Coalition for Change (CCC) ta yi fatali da sakamakon zaben, tana mai cewa "karya ce".

"Mu muka lashe wannan zaben, mu ne shugabanni, mun yi mamakin dalilan da suka sa aka ayyana Mnangagwa a matsayin shugaba," Chamisa, wani ne lauya kuma Fasto da ke jagorantar jam’iyya CCC, ya shaida wa taron manema labarai a Harare babban birnin kasar.

A ranar Laraba da Alhamis ne al'ummar Zimbabwe suka kada kuri'ar zaben shugaban kasa da sabbin ‘yan majalisar dokoki a kasar, yanayin da 'yan adawa suka yi zargin cewa an yi magudi tare da murkushe sakamokon zaben saboda irin jinkirin da aka samu.

Martanin Mnangagwa

"Mun san cewa za mu shiga zabe mai cike da kalubale, muna da kura-kurai sosai a wajen fidda jadawalin zaben da kuma hanyoyi tantance rahoton masu kada kuri'a, baki daya dai yanayin zaben na da matsala, a cewar Chamisa.

Tun da farko a fadar shugaban kasa, Mnangagwa ya kalubalanci wadanda suka yi zargin sake zabensa da aka yi da su garzaya kotu. "Wadanda suke ganin ba a gudanar da zaben nan yadda ya kamata ba, sun san inda za su je," in ji shi.

Zaben ya matukar daukar hankali a fadin yankin kudancin Afirka a wani mataki na nuna goyon baya ga jam’iyyar ZANU- PF ta Mnangagwa wacce ta shafe shekaru 43 tana mulkin kasar da ta yi fama da durkushewar tattalin arziki da kuma zarge-zargen kama-karya.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana damuwarsa a ranar Lahadi game da "kame masu sa ido da rahotannin tsoratar da masu kada kuri'a da kuma barazanar tashin hankali da cin zarafi da kuma tilastawa da aka yi a yayin zaben."

Guterres ya fitar da wata sanarwa inda ya bukaci dukkan bangarorin su ''warware duk wata takaddama da ke tsakani cikin lumana wajen bin kafa doka da hukumomi suka tsara‘’ da kuma warware duk wata matsala ''cikin gaskiya da hikima don tabbatar da cewa sakamakon da aka samu hakikanin muradin al'umma ne''.

Masu sa ido kan zabe daga kasashen waje sun sanar a ranar Juma’a cewa, zaben da aka gudanar ya gaza cimma ka’idojin da aka ware na shiyya-shiyya da na Kasashen duniya kan matakan zabe.

' Dadaddiyar dimokuradiyya '

Tawagar masu sa ido daga kungiyar Tarayyar Turai da kungiyar Commonwealth da kuma kasashe 16 a kudancin Afirka (SADC) sun bayyana wasu jerin abubuwa da suka dau hanakali a zaben, wadanda suka hada da haramta gangamin taro na 'yan adawa da batutuwan da suka shafi rajistar masu kada kuri'a da nuna son kai a kafafen yada labarai na gwamnati da kuma tsoratar da masu kada kuri'a.

Hakan dai bai hana Mnangagwa mika godiyarsa ba “ ina mika godiyata ga kungiyoyi da tawagar masu sa ido daban-daban da suka shaida yadda zabenmu ya gudana ba tare da nuna son kai ba”.

Ya kuma mayar da martani kan sukar da ake yi, yana mai cewa "mun nuna cewa muna da dadaddiyar tsarin dimokradiyya".

“A matsayinmu na kasa mai cin gashin kanta, muna ci gaba da yin kira ga dukkan bakinmu da su mutunta hukumomi da cibiyoyinmu na kasa,” inji shi.

Shugabar hukumar zabe ta kasar ZEC, Justice Chigumba ta ce Mnangagwa ya samu kuri'u sama da miliyan 2.3 yayin da Chamisa ya samu fiye da miliyan 1.9.

Sakamakon samun fiye da rabin kuri'un da aka kada, shugaba Mnangagwa ya yi nasarar tsallake zaben zagaye na biyu a kasar. Hukumar ta ce yawan wadanda suka fito kada kuri'a ya kai kashi 69 cikin dari.

TRT Afrika