Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga mutane a duniya baki daya su nuna kin amincewa da yadda Isra’ila ke kai hare-haren bamabamai kan asibitoci da makarantu da masallatai da kuma coci-coci a Gaza na Falasdinu.
"Dole ‘yan'adam su hana ci-gaba da take dokar kasa da kasa a Gaza," in ji Erdogan a wata wasika da ya rubuta ga Fafaroma Francis ranar Lahadi, yana mai jaddada cewa bai kamata a yi kashe mutane maras laifi da lalata kayayyakin more rayuwa na fararen-hula ba, ko ma a lokacin yaki ne.
Da yake jaddada cewa kisan kai haramun ne a duk addinai da ke da nasaba da Annabi Ibrahim, ya ce dole ‘yan'adam su "daga da muryoyinsu kan kai hare-haren bamabamai a asibitoci da, makarantu da masallatai da coci-coci da bai kamata a lalata ba, ko ma a lokacin yaki ne."
"Matsalolin da muke fuskanta, musamman hare-haren Isra’ila na kan-mai-uwa-da-wabi a Gaza, inda mutuwa ta hanyar yunwa da ke faruwa saboda rashin iya ba da agajin jinkai a cikin azumin watan Ramadana da kuma tasirin yakin Ukraine a duniya wanda a yanzu ya kai shekara ta uku, na bukatar al’ummar duniya su dauki mataki cikin hadin-kai da aiki tare," in ji Erdogan.
Shugaban Turkiyya ya kara da cewar tabbatar da tsaro mai dorewa a Gabas ta Tsakiya ba zai yiwu ba idan ba a warware rikicin Falasdinu da Isra’ila cikin adalci ba.
"Dole a samar da Kasar Faladinsu mai cin gashin kanta wadda ke a dunkule cikin iyakokin shekarar 1967, a duniya a matsayin kasa mai daidaito da sauran kasashen duniya," kamar yadda ya bayyana.
Fafaroma ya gode wa Erdogan kan kokarinsa na samar da zaman lafiya
Shugaban hukumar addinin Turkiyya, Ali Erbas, ya mika wasikar Erdogan yayin da ya ziyarci Fafaroma, wanda ya ce ya gode wa shugaban game da “abin da ya yi."
"Fafaroma Francis ya jaddada cewa shugabanmu daya ne daga cikin shugabanni kalilan da suke aiki tukuru domin zaman lafiya a duniya, kuma da yake da karfin cim ma wannan manufa," in ji Erbas.
Erbas ya kuma ce maudu’in ganarwarsu shi ne "kisan kai, da kuma laifukan cin zarafin bil’adama da Isra’ila ta aikata a Falasdinu."