Wani adadi na Musulmai sun samu hawa kujerun majalisar dokokin Birtaniya sakamakon zaɓen 'yan majalisar dokokin da aka yi duk da nuna ƙyamar Musulunci da ake yi a ƙasar, in ji wata kafar yaɗa labarai ta Musulmai.
Kimanin Musulmai 25 aka zaɓa, wato ƙari daga 19 da aka samu a 2019 a Majalisar Wakilan Birtaniya, in ji kafar yada labarai ta Muslim Network.
Daga cikin 'yan majalisar 25 da aka zaɓa, 18 na jam'iyyar Labour ne, huɗu na Indipenda, biyu kuma na Jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta Conservative da daya na jam'iyyar LD mai rajin kawo canji.
Kafar yaɗa labaran ta intanet ta bayyana cewa goyon bayan da Musulmai masu jefa ƙuri'a suke yi wa Falasɗinawan Gaza ya taka rawa sosai a zaɓen, inda 'yan takarar indipenda biyar da suka haɗa da Musulmai huɗu suka yi nasara.
Shafin ya yi ƙarin haske da cewar akwai Musulmai miliyan 3.4 da ke rayuwa a Birtaniya, kuma zaɓen ya zama wata babbar gaɓa a fagen siyasar ƙasar, yana bayyana yadda tasirin Musulmai ke ƙaruwa a siyasar Birtaniya.
Manyan nasarori
Daga cikin manyan nasarorin da aka samu a jam'iyyar Labour har da ta Sadik Al Hassan a North Somerset, Abtisam Mohamed a Sheffield Central da Zubir Ahmed Glasgow South West.
Sauran da suka fito daga wajen jam'iyyar Labour sun haɗa da Ayoub Khan, Iqbal Mohamed Hussain, Adnan Hussain da Shockat Adam Patel da suka yi nasara a matsayin 'yan takarar indipenda.
Nus Ghani da Saqib Bhatti sun sake lashe zaɓe a jam'iyyar masu ra'ayin riƙau ta Conservative, yayin da Munira Wilson ma ta sake lashe zaɓe a ƙarƙashin jam'iyyar LD.
A zaɓen 2017, kujerun takarar 'yan majalisar dokoki 15 ne kaɗai aka bai wa Musulmai a Birtaniya.