Wasu mutane biyu sun kona Alkur'ani mai girma a wajen ginin majalisar dokoki a birnin Stockholm a kasar Sweden a ranar Litinin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Salwan Momika da Salwan Najem sun yi kwallo da kuma tattaka Alkur'ani, daga nan kuma suka kona shafukansa, kamar yadda suka yi yayin wata zanga-zanga a wajen babban masallacin birnin Stockholm a karshen watan Yuni – abin da ya jawo bacin rai da kuma Allah-wadai daga kasashen Musulmi a fadin duniya.
A 'yan makonnin nan an kona ko kuma lalata shafukan Alkur'ani mai girma a kasashen Denmark da Sweden, wanda hakan ya jawo Allah-wadai daga kasashen Musulmai, inda suka bukaci gwamnatocin kasashen da su hana kona Alkur'anin.
Gwamnatin kasar Denmark a ranar Lahadi ta ce tana kokarin samar da "wata doka" wadda mahukunta za su dogara da ita wajen daukar mataki idan an wulakanta Alkur'ani, ta ce za ta yi hakan ne "idan ta fahimci hakan zai jawo kasar Denmark matsala, ba kawai ta fuskar tsaro ba".
"Abin shi ne muna duba batun a Denmark da kasashen ketare kuma muna aiki don kawar da matsalolin da muke fuskanta," kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Denmark Lars Lokke Rasmussen ya shaida wa manema labarai bayan wata tattaunawa da 'yan majalisa a ranar Litinin.
"Za mu yi haka ne ba domin matsin lamba ba, amma sai don maslaharmu gaba daya ta siyasa," in ji Rasmussen, ya ci gaba da cewa: "Ba za mu zuba ido kawai har sai bayan wani abu babba ya faru ba."
Kasashen sun ce ba sa jin dadin yadda ake kona shafukan Al-Kur'anin, amma kuma sun ce ba za su iya hana yin haka ba, saboda kundin tsarin mulkinsu ya bayar da "damar 'yancin fadin albarkacin baki".
Kodayake yanzu duka gwamnatocin kasashen sun shirin yin sauyi a dokokinsu wanda zai ba mahukunta damar hana kona Alkur'ani a lokutan musamman.
Ita ma gwamnatin Sweden ta ce a wannan wata tana nazari don lalubo hanyar magance matsalar, sai dai 'yan siyasa masu ra'ayin rikau a duka kasashen suna adawa da shirin sauya dokar.