Gwamnatin Taliban a Afghanistan na zuba makudan kudade wajen samar da siminti a matsayin matakinta na farko na samun damar tsayuwa da kafafunta ta fuskar tattalin arzikim inda ta sanya a kalla kwangila uku da kamfanoni masu zaman kansu tun bayan dawo wa mulki a 2021.
Duk da karancin samun tallafi daga kasashen waje, Taliban ta samo hanyar samun kudade, ta dauki matakan yaki da cin hanci da rashawa, da kuma daga darajar kudin kasar, wanda hakan ya hana tattalin arzikinsu rushewa.
A yanzu Taliban na da karfin iko kan Afghanistan sama da duk wata hukuma da aka taɓa yi tun 1970.
A shekaru biyu da suka gabata, an samu raguwar rikici, a yayin da Taliban ta kawar da ƙananan rigingimu, da suka hada da na 'yan ta'addar Daesh a gabashin kasar da kuma kungiyoyn da ke adawa da Taliban a arewaci, kamar yadda Kungiyar Nazari Kan Rikicin Kasa da Kasa ta bayyana.
Wannan yanayin tsaro da aka inganta ya bayar da dama ga ma'aikata da su fadada ayyukansu a bangarori daban-daban na kasuwanci.
Haka kuma, iyaye na bayyana karancin damuwa game da tsaron yaransu a yayin da suke zuwa makaranta, wanda hakan ya kawo daduwar adadin masu zuwa makaranta, duk da haramtawa yara mata zuwa manyan makaranntun sakandire, adadin yara mata a Afghanistan da ke zuwa makarantar firamare ya karu daga kaso 36 zuwa kaso 60.
Sai dai kuma, sakamakon yadda ba su nuna damuwa don tattaunawa kan wannan haramci ba, kungiyar na fuskantar takunkumai, an kuma rufe asusun ajiya a kasashen waje na kasar.
Taliban na gwagwarmayar gudanar da kasuwancin kasa da kasa, kuma ga dukkan alamau ba za su samu kujera a Majalisar Dinkin Duniya a nan kusa ba.
Duk da wadannan kalubale, sun yi kokarin gudanar da manyan ayyuka kamar biyan ma'aikata albashi, sayen lantarki daga kasashen waje, d akuma ware wasu 'yan kudade don gudanar da manyan ayyuka.
Jami'an Taliban sun bayyana cewa yarjeniyoyi uku da kamfanonin kasashen waje da na cikin gida sun hada da sake gina masana'antun siminti a lardunan Parwan, Herat da Kandahar.
A watan Oktoban bara, kamfanin Al Falas da ke da helkwata a Qatar ya karbi kwangilar fadada masana'antar siminti ta Jabal Siraj, tare da hadin gwiwar kamfanin Awfi Bahram na kasar.
Wannan yunkuri na da manufar kara yawan simintin da ake samarwa daga tan 30,000 zuwa 1.5 a shekara, za a samu daduwarsa da ninki miliyan 1.5 a shekara, kuma hakan zai kara yawan kudaden samar da kayan da ninki 50.
"An sanya hannu kan kwangilolin Herat da Kandahar tare da kamfanoni da masu zuba jari na cikin gida, amma kwangilar Jabal Sirajkuma a bawa kamfanin Qatar shi kadai," Humayoon Afghan, kakakin mai'aikatar ma'adanai da albarkatun mai.
"Dukkan su za su zuba jarin kusan dala miliyan $450... Kuma wadannan kwangiloli na tsawon shekaru 30 ne. Kowacce masana'anta za ta samar da kusan tan biliyan 1.5 na siminti a shekara"
Ya kara da cewa Afghanistan ta mallaki dukkan kayan da ake bukata don samar da siminti, ciki har da kwal.
A yanzu haka, Afghanistan na kashe daruruwan miliyoyin dala don shigo da siminti a kowacce shekara.
Amma kuma, da zarar kamfanonin uku sun fara aiki, kasar za ta samar da simintin da take bukata. Maimakon ta dinga shigo da shi, watakila ma Afghanistan ta fara fitar da siminti zuwa kasashen waje.
Manazarta na cewa wannan zai taimakawa Afghanistan sosai wajen zama da kafarta a sha'anin kudade.
"Za mu iya cewa a kowacce rana, Afghanistan na samar da tan 900 na siminti, wanda ba zai biya kaso daua bisa goma na bukatar sa da ake yi a kasar ba.
Idan masana'antun suka fara aiki sanna aka samu zuba jari, za a samu siminti mai arha a kasuwanni." in ji Nazak Mir Zyarmal, masanin tattalin arziki dan kasar Afganistan yayin tattaunawa da TRT World.
"Zai zama mun daina shigo da siminti, kuma Afghanistan za ta dogara ga kanta ba tare da dogaro kan kasashen waje ba."
Afganistan na tutiya da yawaitar sinadarin coal da tale da shi a kasar, wanda ke shimfide a yankin Jurassic da ya faro daga lardunan arewaci na Takhar da Badakhshan zuw atsakiyar kasar sannan suka baza zuwa bangaren yamma a jihar Herat.
Ana amfani da coal a matsayin makamashi wajen samar da siminti, saboda ana bukatar makamashi da yawa wajen samar da siminti. Injina na kona garin coal inda ake amfani da da 450g na kwal don samar da siminti mai yawan giram 900.
A yanzu haka, masana'antun siminti na Ghori a lardin Baghlan da na Jabal Siraj a lardin parwan ne suke aiki a kasar kuma ba sa samar da yadda ake so.
Zyamar ya ce "A yanzu ana kai siminti Afghanistan daga tajikistan, Iran da Pakistan, duk da cewa Afganistan ta riga wadannan kasashe samar da kamfanonin siminti."
Ya fada wa TRT World cewa "Abin takaici, wadannan masana'antu suna aiki a cikin wannan yanayi na gaza samar da simintin da ake so kuma an ƙi inganta su, gwamnatocin da suka biyo baya sun yi biris da su tare da kin habaka ƙarfin su."
"Sakamakon haka, a yayin da bukatar siminti ke daduwa a Afghanistan, ya zama dole ta shigar da su daga kasashen ketare don biyan bukatarta."
Kokarin wadatar da kanta
A ranar 25 ga Maris jami'an ma'aikatar ciniki ta Pakistan suka zo Kabul don fara tattaunawa don habaka alakar kasuwanci, watanni bayan tabarbarewar alakat tsakanin kasashen biyu makota.
Tsawon shekaru, Pakistan ta zama babbar kawar kasuwancin Afghanistan.
Amma tabarbarewar rikicin 'yan bindiga a kan iyakoki ya sanya Pakistan dakatar da kasuwanci, duk da ma Islamabad ta nuna ba ta goyon bayan Taliban.
Pakistan ta zargi gwamnatin rikon kwarya ta Afghanistan da taimaka wa 'yan tawayen Tahreek-e-Taliban-e-Pakistan (TTP), wada ta yi ikirarin na amfani da yankunan Afghanistan su kai hari kan Pakistan.
Kabul sun musanta wannan inda suka ce ba sa bayar da dama ga wani ya yi amfani da yankin Afghanistan don kaiwa Pakistan hari.
Dadin dadawa, Pakistan, tare da Iran, sun kori dubunnan daruruwan 'yan gudun hijirar Afghanistan.
Gwamnatin Taliban ta magance cin hanci a cibiyoyin kwastan, wanda ya kara yawan kudaden shigar da kasar ke samu sama da na gwamnatin da ta gabata.
Sai dai kuma, kudaden shigar da suke samu ya ta'allaka ne kusan kan fitar da coal da suke yi zuwa Pakistan, wanda ya ragu a karshen 2023 saboda ta'azzarar rikici a kan iyakokinsu.
"Zuba jari a bangaren samar da siminti ba zai sauya al'amarin ba saboda ana samun siminti a kowacce kasa. Sai dai kuma, a cikin gida, hakan zai amfani Afghanistan sosai ta hanyoyi da dama," in ji Matiullah Faeeq, Babban Mai Bincike a Cibiyar Biruni.
Ya fada wa TRT World cewa "Afganistan ta kasance a cikin yaki na tsawon shekara 45, kuma sake gina kayan more rayuwa kamar hanyoyi, gadoji, da gidaje ne ya kamata a baiwa fifiko."
"A yanzu haka, Afganistan na shigar da mafi yawan simintin da take bukata. Ana sa ran wadannan masana'antu na siminti za su bawa Afganistan damar fitar da siminti zuwa kasashen waje, za su rage gibin d atake da shi na kasuwanci."
Kari kan hakan, duk wani zuba jari daga kasar waje a Afghanistan alama ce ta amince wa da kasar. in ji Faeeq, yana mai kira ga masu zuba jari na cikin gida da waje kan su samar da ayyukan yi a sauran bangarori a kasar.
Afganistan na cikin yanayin sauyi, kuma a matsayin kasa mafi rashin ci gaba a duniya, na bukatar zuba jari sosai a bangaren zuba jari don bunkasa tattalin arziki, kakkabe talauci da samun cigaban zamantakewa.
"Siminti na da muhimmanci a bangare gine-gine, gina gadoji, hanyoyi, madatsun ruwa a sauran kayan more rayuwa. Wadannan ayyuka za su bayar da dama a kula a harkokin sufuri, makamashi da samar da ruwan sha," in ji Faeeq.
"Ana sa ran cigaban birane a Afghanistan zai ci gaba karu wa daga kaso 26 a 2022. A yayin da jama'a suke kaura zuwa birane, akwai bukatar gidaje da shagunan gudanar da kasuwanci."