Har yanzu da take cikin ta Majalisar Dinkin Duniya, babu wata kungiya da ta amince da gwamnatin Taliban. / Hoto: AFP

Shekara biyu da suka gabata a ranar 15 ga Agusta, Taliban ta sake karbe iko da Afganistan, inda ta fara firgita jama'a da tattalin arziki da fagen siyasar kasar.

Taliban ta karbe iko da Afganistan bayan da sojojin Amurka suka janye daga kasar da ta afkawa tsawon shekara 20.

A yayin cika kwana 730, har yanzu Afganistan na fuskantar kalubale da dama, da suka hada da kare hakkokin dan adam da kokarin dawo da alaka a kasashen duniya.

Har yanzu da take cikin ta Majalisar Dinkin Duniya, babu wata kungiya da ta amince da gwamnatin Taliban.

Babu wata kasa da ta kulla alakar diflomasiyya da Taliban, duk da cewa wasu kasashen sun dan kulla alaka da sabuwar gwamnatin.

Kafin Taliban ta karbe iko da Afganistan, kasar ta dogara ne kan taimako daga kasashen waje da tallafin kungiyoyin kasa da kasa.

Kasar da ta ke fuskantar tashin gwauron zabin kayan masarufi, tana kuma cikin tsananin bukatar habaka tattalin arziki da ta sanya su fara tattaunawa da kasashe irin su China da Kazakhstan.

Kasar da ake wa lakabi da "Zuciyar Asiya", Afganistan ba ta da iyaka da teku, tana da girman murabba'i 652,864, ta yi iyaka da kasashen Pakistan da Turkmenistan da Iran da Uzbekistan da Tajikistan da kuma China.

Babban birninta Kabul na nan a kan hanyar kasuwancin Tsakiyar Asiya da Kudancin Asiya, wanda ya zama waje mai matukar muhimmanci kusan rabin yadda Istanbul yake tsakanin Gabas da Yamma.

Taliban kuma ta sanya idanuwanta kan Turkiyya inda take sha'awar zuba jarin Turkiyya a Afganistan.

Ma'aikatar Ciniki da Masana'antu ta Afganistan ta bayyana cewar abubuwan da kasar take fitarwa zuwa Turkiyya sun hada da gyadar almond da dardumai da alhariri da fatu da kiraga da auduga da busasshen apricot.

Domin habaka kasuwanci da cudanya da kasashe makota, mataimakin Firaminista Mai Kula da Harkokin Tattalin Arziki, Mullah Abdul Ghani Baradar, a kwanakin baya ya gana da Ministan Ciniki na Turkiyya Farfesa Omer Bolt inda suka tattauna yadda za su saukaka wa juna gudanar da kasuwanci a tsakanin su.

Kalubalen tsaro

A cikin gida, Taliban na murkushe kungiyoyin ta'adda, kamar Daesh. Kuma ta yi kokarin yaki da cin hanci da rashawa.

Duk da habaka tsaron kasa, gwamnatin Taliban za ta dauki tsawon lokaci da ayyuka da dama don inganta rayuwar 'yan kasar.

Daya daga cikin manyan matsalolin Afganistan shi ne batun 'yancin mata, wanda ke janyo wa mata wahala ko gaza ganinsu a rayuwar yau da kullum ta bainar jama'a, inda haramcin da ake saka musu ke hana su zuwa makarantu, dakunan gyaran jiki da filayen shakatawa da ke Kabul.

Wannan ya daba wa alkawarin Taliban na farko wanda ta bayar da tabbacin mata za su taka rawa a cikin al'umma, kuma za a kare hakkokinsu.

Dokar da shugaban Taliban Mullah Haibatullah Akhundzada ya fitar ta wajabtawa mata rufe jikinsu gaba daya a waje, sannan an dakatar da karatu mai zurfi da suke yi da kuma aiki karkashin kungiyoyin da ba na gwamnati ba.

A lokacin da aka cika shekara biyu da sake karbar mulkin Taliban, kokarin kasar na sasantawa da kasashen duniya na fuskantar makoma mai cike da rudani, inda kuma 'yancin dan adam a kasar ke fuskantar kalubale.

TRT World