Mazauna yankin da kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun zargi jami'an tsaron Indiya da aikata ta'asa a yankin Kashmir da ke karkashin ikon kasar/Hoto: Reuters  

Firaiministan Indiya Narendra Modi na ci gaba da balaguron yaƙin neman zaɓe a ƙasar, sai dai wannan ne karon farko tun shekarar 1996 da jam'iyyarsa ta Bharatiya Janata BJP ta ki zuwa neman zabe a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon ƙasar.

A maimakon hakan, manyan 'yan takarar kujeru uku a yankin da musulmai ke da rinjaye ne suka fito a jam'iyyun ƙasar masu karfi wato National Conference da jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Za su fafata da juna, sai dai su dukkansu suna adawa da jam'iyyar BJP mai ra'ayin kishin addinin Hindu kana za su haɗa kai da jam'iyyar ƙawancen 'yan adawa karkashin jam'iyyar Congress.

Yankin Himalayan da ke fama da taƙaddama kan ikonsa, wanda Indiya da Pakistan suka yi mulkin wani bangarensa bayan samun 'yancin kai daga Birtaniya a 1947.

Masu sharhi da jam'iyyun adawa sun bayyana cewa BJP ta yanke shawarar tsallake zuwa neman zaɓe a yankin Kashmir ne saboda akwai yiwuwar sakamakon da a samu zai saɓa da manufar Modi na samar da zaman lafiya da kuma haɗin kai a yankin da ya samu cin gashin kansa a shekarar 2019 kana ya mayar da shi karkashin ikon New Delhi.

Jam'iyyar BJP, tare da kawayenta, za su yi nema takara a duk faɗin Indiya kuma ana hasashen za su lashe mafi yawan kujeru 543 na majalisar dokoki, bisa ga manufarta kan tsarin Hindu.

"Me yasa basu halarci zaben ba?" Omar Abdullah, shugaban jam'iyyar National Conference kuma tsohon babban minista a Jammu da yankin Kashmir ya aza ayar tambaya.

''A bayyane yake cewa akwai rata sosai tsakanin abubuwan da jam'iyyar BJP ta ke ikirarin ta yi da kuma gaskiyar abin da ke ƙasa," in ji Abdullahi a yayin wata zantawa da aka yi da shi a gidansa da ke babban birnin Kasmir na Indiya, Srinagar.

Modi ya ce shawarar da ya yanke a shekarar 2019 ta kawo zaman lafiya a yankin Kashmir bayan shafe tsawon shekaru da dama ana zubar da jini kana ya ce nan ba da daɗewa ba zai samar da hannayen jari da ayyukan yi.

Ministan cikin gida na tarayya Amit Shah ya goyi bayan matakin gwamnatin inda ya ce yanzu haka matasa suna rike da kwamfutar tafi-da-gidanka a hannunsu maimakon duwatsun da suke jifan jami’an tsaro da shi a baya.

A wani bangare na wannan yunkuri, an raba jihar Jammu da Kashmir da ke karkashin ikon Indiya zuwa yankuna biyu na gwamnatin tarayya - Yankin kwarin Kashmir da musulmai ke da rinjaye da filayen Jummu wanda mabiya addinin Hindu suka mamaye sai kuma tsaunukan Ladakh da mabiya addinin Buddah suka mamaye.

A wannan lokacin ne gwamnati ta sanya dokar ta-baci a yankin Kashmir, yanayin da ya kai ga tsare kusan dukka shugabannin yankin ciki har da Abdullah har na tsawon wasu watanni.

Ravinder Raina, shugaban jam'iyyar BJP a Kashmir, ya ce matakin da jam’iyyar ta dauka na tsallake zabe a jihar na daga cikin wani muhimmin bangare na dabarunta, kodayake dai bai yi wani takamaimam karin bayani kan hakan ba.

"Jam'iyyar BJP ba za ta yi faɗa ba, amma za ta goyi bayan ɗan takarar da zai yi aiki tukuru don samar da zaman lafiya da walwala da kuma samar da haɗin kai da dimokuradiyya," a duka kujeru uku da ake da su, in ji shi, har yanzu BJP ba ta sanar da wanne daga cikin jam'iyyun za ta marawa baya ba.

Rashin gamsuwa da nuna wariya

Wata tattaunawa da aka yi da mazauna yankin sama da mutum goma sha biyu, da shugabannin siyasa da jami'an tsaro da kuma masu sharhi a Kashmir da New Delhi na nuni da cewa akwai rashin gamsuwa da nuna wariya da ake ci gaba da fuskanta a yankin Himalayan da ke jibge da sojoji.

Indiya na zargin cewa Pakistan na goyon bayan tayar da ƙayar baya ne a Kashmir yayin da ita kuma Islamabad ta ce tana ba da goyon bayanta ne kawai ga al'ummar yankin.

Abdul Hameed, mai shekaru 50 da ke da kantin sayar da kayan sawa a garin Pulwama kusa da Srinagar, ya ce tun daga 2019 gwamnatin tarayya ta ke ɓoye ainihin halin da ake ciki a Kashmir.

Shekaru da dama, mazauna yankin da kungiyoyin kare hakkin bil'adama na zargin jami'an tsaron Indiya da cin zarafin al'ummar Musulmai.

Gwamnati ta ce laifukan cin zarafi boyayyayun ayyuka ne da ake yi kana tana hukunta duk wani soja da aka samu da laifin take hakkin ɗan'adam.

Bayanan rundunar sojin Indiya sun nuna cewa akwai sama da ‘yan bindiga 100 a yankin, wadanda ake zargi da kai hari kan jami’an tsaro da ma’aikata daga wasu sassan kasar.

''‘Yan bindiga sun kashe wani sojin sama a wani hari da suka kai wa ayarin motocin dakarun soji a ranar Asabar,'' in ji bayanan rundunar.

''Rashin tsarin zabe a yankin na zama manuniya kan yadda abubuwan da ke tafiya a can ba sa bayyana zahirin ainihin abin da ke faruwa,'' a cewar Sheikh Showkat Hussain, wanin farfesa a fannin shari'a a Srinagar.

Ya ƙara da cewa "Ya kamata 'yan jam'iyyar BJP su dauki (wannan zabe) a matsayin kuri'ar raba gardama a gare su. Amma da alama a tsorace suke."

A babban zaben watan Mayu na 2019, BJP ta fafata a takarar kujeru uku a Kashmir, inda ta rasa su ga jam'iyyar Abdullah ta National Conference.

A bana kuma, BJP za ta yi takarar kujeru biyu da ke Jammu da kuma daya a Ladakh, wanda duk ta lashe su a 2019.

Mehbooba Mufti, shugaban jam'iyyar PDP, yana takara ne daga mazabar Anantnag-Rajouri, wanda mutane da dama suka imanin cewa zai zama wata dama ga BJP ta samu kafar shiga yankin Kashmir a wannan zaben.

A 2022 ne hukumar zabe da gwamantin tarayya ta nada ta canza iyakokin mazabu a Kashmir da Jammu.

Mazabar gudumar Anantnag na Kashmir, da ke da kusan kuri'un al'ummar musulmai miliyan 1.6 a 2019, ya samu karin kusan kuri'u mabiya addinin hindu miliyan daya daga gundumomin Poonch da Rajauri na Jammu.

Mufti ta shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa ta hanyar haɗa kuri'un zaben dukka, gwamantin Modi tana ''canja tsarin tattara sakamakon kuri'u ne''. in ji ta.

A cewarta BJP tana son ''ta rage tasiri da kuma karkatar da mulki daga hannun musulmai musamman 'yan kashmir.''

Jam'iyyar Abdullah ta National Conference ta yi ikirarin cewa a daukin matakin sake fasalin gundumar don bai wa BJP "damammaki".

Amma duk da haka, har yanzu ba su fitar da ɗan takara ba, wanda ke nuna yadda abubuwa rincaɓe wa BJP,'' in ji Abdullah.

Ko da yake dai, shugaban jam'iyyar BJP Raina ya ce sake fasalin ya sanya mazabu su zama wakilai na yankin.

Reuters