Kuka mai daga hankali da Nomina Khatoon 'yar Rohingya ke yi a yayin da take raka masu jana'izarta danta dan wata biyar ya dinga ratsa iskar cikin dare yana kai wa ga kunnuwan mutane da dama da ke kewayen.
Ta kasance daure cikin ankwa yayin da tawagar jami'an 'yan sanda ke jan ta a kasa a kan titunan birnin Jammu na arewacin Indiya, mai nisan kilomita 600 daga babban birnin kasar New Delhi.
Kamar Khatoon wacce take cikin shekaru 30, haka ma jaririnta ya kasance a tsare a wani sansani, da aka kiyasta cewa ana tsare da Musulman Rohingya 270 a ciki, wadanda ke neman mafaka bayan da aka tursasa musu tserewa daga kasarsu.
Khatoon ta haifi danta a sansanin bayan da aka tsare ta ranar 5 ga watan Maris na 2021, tare da sauran 'yan gudun hijira.
'Yan gudun hijirar sun yi kokarin balle sansani tare da tserewa daga cikinsa ranar 18 ga watan Janairu, sakamakon mummunan yanayin da suke ciki da zargin rashin samun abinci da sauran muhimman kayan bukatun rayuwa.
An zargi dakarun tsaro da yin harbi da fesa hayaki mai sa hawaye don ladabtar da 'yan gudun hijirar masu cike da fushi, lamarin da ya sa mutane da dama suka raunata, a cewar Kungiyar Kare Hakkin 'Yan Rohingya (ROHRIngya).
An yi zargin cewa jaririn Khatoon ya rasu ne sakamakon shakar hayaki mai sa hawaye. A wani bidiyo da kungiyar ta wallafa a Twitter an ga Khatoon daure cikin ankwa a cikin masu kukan mutuwar dan nata.
"Akwai wasu ma da dama da suka jikkata da suke cikin halin mutu kwakwai rai kwakwai. Za su rasa rayukansu," a cewar kungiyar ROHRIngya a Twitter.
"Hukumomi sun yi wa mutane da dama dukan kawo wuka. An kama 'yan gudun hijira biyar, mata biyu da maza uku. Sannan ana musguna musu sosai."
Koushal Kumar, jami'in da ke kula da sansanin da ake tsare mutanen, ya karyata batun mutuwar jaririn a lamarin.
Ya shaida wa TRT World cewa "Sai da 'yan sanda suka shiga lamarin wajen ceto jami'ansu uku da 'yan gudun hijirar suka yi garkuwa da su." "Sannan 'yan Rohingyan sun ji wa 'yan sanda da dama rauni sakamakon jifansu da suka dinga yi da duwatsu.
A kiyasin da gwamnatin Indiya ta yi, kusan 'yan Rohingya 40,000 ne ke zaune a jihohi daban-daban na Indiya, kasar da ta hada iyaka mai tsawon kilomita 1,643 da Myanmar.
Sai dai, Kungiyar Human Rights Watch ta ce 'yan Rohingya 20,000 ne kawai aka yi wa rajista da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya. Mafiya yawan 'yan gudun hijirar sun shiga Indiya ne daga tsakanin 2012 zuwa 2016 daga Myanmar.
Ana zargin gwamnatin masu ra'ayin addinin Hindu ta Firaminista Narendra Modi da kama Musulman Rohingya 'yan gudun hijira tare da tsare su ba tare da ba su damar samun taimakon shari'a ba.
Wasu abubuwa da suka faru a baya-bayan nan sun kara tabbatar da zarge-zargen.
A ranar 24 ga watan Yulin, sashen yaki da ta'addanci na rundunar 'yan sanda a Jihar Uttar Pradesh ya kama 'yan Rohingya 74 a yayin wani samame da aka yi a gundumomi shida.
Wani babban jami'in 'yan sanda Prashant Kumar, ya ce mutanen da aka kama din sun hada da mata 16 da yara biyar.
Sai dai ba a san in da ake tsare da wadannan 'yan Rohingyan ba.
Rura wutar kiyayya
Indiya ba ta cikin kasashen da suka sa hannu a kan Yarjejeniyar 'Yan Gudun Hijira ta MDD ta 1951, wacce ta lissafto 'yancin 'yan gudun hijira da alhakin da aka dora wa kasashe don ba su kariya.
Masu fafutuka sun ce kiyayyar da kungiyoyin masu tsaurin ra'ayi da na Bharatiya Janata Party (BJP) ta Firaminista Modi ke nuna wa 'yan Rohingya na uzzura wutar kiyayyarsu a wurare da dama.
Sannan kuma a Jihar Jammu, wani yanki da al'ummar mabiya Hindu suka fi yawa a yankin Jammu da Kashmir, kungiyoyin masu tsaurin ra'ayi sun shafe shekaru suna rikici da 'yan gudun hijira.
A watan Fabrairun 2017, wani lauya kuma mamba na Jam'iyyar BJP, ya je kotu yana neman gwamnati ta mayar da dukkan "'yan gudun hijirar da ke kasar ba bisa ka'ida ba" daga Myanmar da Bangladesh zuwa wasu wuraren.
A yankin Jammu ne aka fara zafafa kiyayyar 'yan Rohingya - in da can ne 'yan gudun hijira 7,000 ke samun mafaka - in da har kungiyoyin masu tsananin ra'ayin addinin Hindu suka dinga jagorantar fafutukar korar 'yan Rohingya ta karfi da yaji.
Wasu kungiyoyin 'yan kasuwa ne suka dinga rura wutar fafutukar, wadanda suke kyamatar 'yan Rohingya da kiran su "masu aikata miyagun laifuka da masu safarar kwayoyin da kasarsu ma ta yi watsi da su."
Har wata barazana suka yi ta zuga mutane da "su dinga kashe" 'yan Rohingya a duk in da suka gans u idan dai har gwamnati ta ki mayar da su kasarsu.
Jammu da yankin Kashmir na Indiya jiha daya ne a baya har sai 2019 da aka cire mata matsayinta na musamman ta koma karkashin gwamnatin tarayya a Delhi.
A shekarar 2017, gwamnatin tarayya ta nemi dukkan gwamnatocin jihohi da su nemo tare da mayar da dukkan "yan gudun hijirar da ke zaune a kasar ba bisa ka'ida ba", ciki har da 'yan Rohingya.
Gwamnatin tarayyar ta yi ikirarin cewa "'kungiyoyin ta''addanci sun fi saukin amfani da 'yan gudun hijirar da ke zaune ba bisa ka'ida ba wajen sanya su a cikinsu," batun da shugabannin Jam'iyyar BJP suka goyi bayansa.
A watan Fabrairun 2021, wata kotu ta bai wa gwamnatin umarnin gaya mata matakan da take dauka ko wadanda za ta dauke kan batun "'yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba."
Wata guda bayan nan, 'yan sanda sun tsare kusan 'yan Rohingya 170 – da suka hada da mata da yara – daga bisani da suka tsare su a sansani a Jammu.
Murshid Alam, wani dan Rohingya da ke zaune a wani waje daban a Jammu, ya ce an shafe shekaru ana kama mutane da tsare su.
"Sannan akwai yanayi daban-daban da aka tsare kananan yara su kadai a sansanonin, saboda 'yan sanda sun dauke iyayensu. An raba iyaye da 'ya'yansu. Akwai wani lamari ma da ake raba ma'aurata," kamar yadda Alam ya shaida wa TRT World ta wayar tarho.
Rayuwa cikin fargaba
A wani sansani na yan Rohingya da ke garin Nuh a Jihar Haryana da ke iyaka da Delhi, Hasan yan cikin tashin hankali yayin da yake magana da 'yan uwansa 'yan Rohingya da ke sansanin Jammu.
"An fi shekara biyu yanzu, kuma har yanzu mutanenmu ba su dawo ba... (tun lokacin) kusan 'yan gudun hijira 10 zuwa 12 ne suka rasa rayukansu a tsare, hudu kuma suka yi batan dabo," a cewar Hasan, wanda bai fadi cikakken sunansa ba.
Wani rahoton kungiyar ROHRIngya ya ce an tsare 'yan gudun hijira da dama ba bisa ka'ida ba daga tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022.
Sophica, wata 'yar Rohingya da ita ma ke zaune a Nuh da ba ta fadi cikakken sunanta ba, ta kusa fashewa da kuka lokacin da take bayar da labarin irin rashin tausayi da azabar da ake ganawa danginta da ke tsare a Jammu.
"Kusan mutum 10 zuwa 15 ne da suka hada da mata da yara aka ji wa rauni ranar 18 ga watan Yuli. An ga bidiyoyin da ke nuna yadda ake dukan mata cikin rashin tausayi. Akwai wanda aka lalata masa kafa saboda duka. 'Yan sanda sun yi ta dukan mutane har da masu ciki da tsofaffi da marasa lafiya," ta kara da cewa.
Shama Khatoon, wacce ake tsare da 'yarta da surukinta a sansanin a Jammu tare da 'ya'yansu biyu, ta ce "ana barin mata masu shayarwa da yunwa. Haka ma jariran nasu.
"Ba a barin kowa ya gana da wadanda ake tsare da su din. Ko audugar mata ba za mu iya taimaka wa mata da ita ba. Sai dai su yi amfani da tsumma mai datti wanda hakan ke jawo musu cututtuka.
Ta ce fursunonin da ke sansanin Jammu na fama da yunwa don abincin da hukuma ke ba su dan kadan ne. "Wasu har ganyen bishiya suke ci don su rayu," ta kara da cewa.
A yanzu haka fargabar kar a kai su kurkukun ta ishi 'yan gudun hijirar Rohingya da ke Nuh, da yawansu ya kai mutum 1,900, in da suke fama da matsalolin rashin abinci da ruwa.
Hasan, ya kuma bayyana cewa a ranar 13 ga watan Yuli, 'yan sanda a garin nuh sun ce shi da sauran mutanen da ke wajen duk za a aike da su sansanin Jammu.
"Tun daga lokacin ba ma iya bacci cikin nutsuwa. Muna zaune cikin kunci da fargabar yadda kaddararmu za ta kasance."
Ita ma Sophica cikin kuka ta ce, “Wa ya sani ma ko idan kuka sake zuwa nan ba za ku tarar da mu ba... Ba mamaki mu kasance a wannan kurkukun."