Har yanzu ana ci gaba da fafatawa tsakanin sojojin Isra'ila da dakarun Hamas. Hoto/Reuters

1435 GMT — Jarirai bakwaini 36 suna cikin hatsari a asibitin Gaza, tuni uku sun mutu

Jarirai bakwaini 36 a asibitin Al Shifa na Gaza na cikin yanayin mutu kwakwai rai kwakwai, a cewar ma'aikatan kiwon lafiya, waɗanda suka suka ce babu wata tabbatacciyar hanyar taimaka musu duk da kokarin da Isra'ila ta yi na samar da kwalaben da za a kwashe su a ciki.

Uku daga cikin jarirai bakwaini 39 sun riga sun mutu tun lokacin da janareton babban asibitin Gaza ya daina aiki saboda ƙarewar fetur a karshen mako, wanda shi ne ke samar da wutar lantarkin da ke sa wa kwalaebn ajiye su suke aiki.

An yi sa'a har yanzu 36 da ba su mutu, ba mu rasa ko daya daga cikinsu a cikin dare daya ba," Dr Ahmed El Mokhatallali, wani likitan tiyata, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho daga Al Shifa. "Amma duk da haka hadarin yana da yawa ... za mu iya rasa su."

1417 GMT — Asibitoci 25 cikin 35 na Gaza sun daina aiki saboda yaƙin Isra'ila - Hamas

Wani jami'in Hamas ya ce harin bama-bamai da Isra'ila ta kai a Gaza ya sanya 25 daga cikin asibitoci 35 na yankin da aka yi wa ƙawanya sun daina aiki.

Osama Hamdan wani jami'in kungiyar Hamas da ke birnin Beirut, ya shaida wa taron manema labarai a babban birnin kasar Labanon cewa "Hare-haren Isra'ilan sun kuma lalata gine-ginen gwamnati 94 da makarantu 253."

1420 GMT Hezbollah ta ce ta raunata sojojin Isra'ila a kan iyaka

Kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta ce ta kai hari ga sojojin Isra’ila a sansaninsu da ke kusa da kan iyaka inda ta raunata su.

Kungiyar ta Hezbollah na taya Hamas yakin da take yi da Isra’ila.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare Gaza inda ta kashe sama da mutum 11,200.

0935 GMT — An binne gawawwaki 179 a cikin kabari guda a harabar asibitin Gaza

Daraktan asibitin Gaza mafi girma a ranar Talata ya ce mutum 179, daga ciki har da jarirai da marasa lafiya wadanda suka mutu a dakin kula da marasa lafiya an binne su a cikin kabari guda a harabar asibitin.

“An tilasta mana rufe su a kabari daya,” in ji daraktan Asibitin Al-Shifa Mohammad Abu Salmiyah inda ya ce akwai jarirai bakwai da marasa lafiya 29 wadanda ke dakin marasa lafiya masu tsananin bukatar kulawa na daga cikin wadanda aka binne.

Zuwa yanzu Isra'ila ta kashe sama da mutum 11,180 a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba. / Hoto: Reuters

Wani dan jarida wanda ke a cikin asibitin da ke hadin gwiwa da kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce akwai gawawwaki a ta ko ina a asibitin wadanda suka soma rubewa.

0848 GMT — Isra'ila ta sake kashe Falasdinawa shida a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Isra’ila ta sake kashe Falasdinawa shida a hare-haren da take kaiwa cikin dare a Gabar Yamma da Kogin Jirdan da Isra’ilar ta mamaye, kamar yadda kafar watsa labarai ta Falasdinawa ta bayyana a ranar Talata.

Falasdinawa biyar aka kashe a birnin Tulkarem a wani harin sama da Isra’ila ta kai wanda kuma ya raunata mutum tara, inda mutm uku ke cikin hali mai tsanani, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinu ya tabbatar.

Haka kuma akwai karin Bafalasdine guda da Isra’ila ta kashe a kusa da birnin Hebron, inda Isra’ilar ta yi ikirarin ya yi niyyar kai musu hari da wuka.

0750 GMT — Lauyoyin Falasdinawa sun shigar da Isra'ila kara a Kotun ICC

Lauyoyin wadanda hare-haren Isra'ila suka fadamawa a Gaza sun shigar da kara a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC da ke birnin Hague na Netherlands.

Wakilin jama'ar Gaza a kotun ICC wato Gilles Devers da wasu mutum hudu da suka masa rakiya domin kai korafin sun bayyana cewa Isra'ila ta aikata laifukan yaki a kan Gaza wadanda suka hada da kisan kare-dangi.

Isra'ila ta kashe sama da mutum 11,180 a Gaza wadanda akasarinsu yara ne tun daga 7 ga watan Oktoba.

AA
AFP
AP
Reuters
TRT World