1300 GMT — Sarkin Qatar ya jaddada bukatarsa ta dakatar da yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza
Sarkin Qatar Sheikh Tamim Bin Hamad Al Thani ya jaddada yunƙurin ƙasarsa na dakatar da yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza, yana mai bayyana yanayin da ake ciki a matsayin abin takaici, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Qatar ya ruwaito.
A yayin ganawarsa da shugaban kasar Poland Andrzej Duda a birnin Warsaw, sarkin ya tabbatar da cewa Qatar na neman dakatar da yakin ne ta hanyar lalubo bakin zaren warware rikicin, da dakatar da fada da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.
Halin da ake ciki a yankin yana da ban tausayi da wahala, kuma muna bukatar kokarin duniya don dakatar da wannan yaƙi, in ji shi.
Sheikh Tamim ya isa birnin Warsaw daga birnin Astana na kasar Kazakhstan inda ya halarci taron kwanaki biyu na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai.
1120 GMT — An tono gawarwakin Falasɗinawa 10 a ƙarƙashin a ɓaraguzai a kudancin Gaza
An kwaso gawarwakin Falasdinawa akalla 14 daga ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da ke Rafah a kudancin Zirin Gaza, kamar yadda majiyoyin lafiya suka shaida wa Anadolu a ranar Juma'a.
Majiyar ta ce sun karbi gawarwakin Falasdinawa 14 daga yankunan yammacin birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza.
Majiyoyin kiwon lafiya sun kara da cewa akalla guda 10 daga cikin wadancan gawarwakin sun ruɓe ne kuma ba a tantance su ba.
Isra'ila, wadda ta yi fatali da kudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci a tsagaita wuta cikin gaggawa, ta fuskanci tofin Allah tsine daga kasashen duniya a daidai lokacin da take ci gaba da kai munanan hare-hare kan Gaza tun bayan harin da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta kai a ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Fiye da Falasdinawan 38,000 ne aka kashe tun daga lokacin, akasari mata da yara, yayin da wasu sama da 87,000 suka jikkata, a cewar hukumomin lafiya na yankin.
Kusan watanni tara da fara yakin Isra'ila, yankunan Gaza da dama sun koma kufai a cikin yanayi na takunkuman da aka sanya wa zirin na hana shigar da abinci da ruwa mai tsafta da kuma magunguna.
Ana tuhumar Isra'ila da aikata kisan kiyashi a kotun kasa da kasa, hukuncin da aka yanke na baya-bayan nan ya ba da umarnin dakatar da aikin soji a kudancin birnin Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan guda suka nemi mafaka daga yakin kafin a mamaye shi a ranar 6 ga watan Mayu.
0327 GMT — Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a Gaza, ta kashe ƙarin Falasɗinawa
Wasu hare-hare da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai a gidajen biyu a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasɗinawa huɗu, cikinsu har da mata biyu.
Jami'ai a Asibitin Al-Awda da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat a tsakiyar Gaza sun tabbatar da kai musu “shahidai biyu da mutane da dama da suka jikkata bayan hari ta sama da aka kai a gidan iyalan Sarraj da ke sansanin Nuseirat."
Hukumar Bayar da agaji ta Gaza Civil Defence Agency ta fitar da wata sanarwa da ke cewa jami'anta sun gano gawawwaki biyu na wasu mata sannan sun tono mutane da dama daga ɓaraguzai a gidansu da ke Bardawil a yankin Daraj inda suka kai su asibiti, bayan jiragen yaƙin Isra'ila sun yi masa luguden wuta.
2049 GMT — Hamas ta ce ta mayar da martani mai kyau ga Isra'ila kan shirin zaman lafiya na Biden
Wani jami'in kungiyar Hamas ya bayyana cewa, kungiyarsa ta mayar da martani mai kyau ga sabon kudurin tsagaita wuta a Zirin Gaza tare da sanar da masu shiga tsakani cewa a shirye suke da duk wata shawara da ta dace da bukatun al'ummar Falasdinu.
Ali Baraka shugaban sashen hulda da jama'a na Hamas da ke kasashen waje ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa, bangarorin Hamas da Falasdinawa a shirye suke ga duk wani shiri da zai biya bukatun al'ummarFalasdinu.
A cewar Baraka, bukatun al'ummar Falasdinu sun hada da "tsagaita wuta na dindindin, da janyewar sojojin Isra'ila daga Zirin Gaza gaba daya, da mayar da mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa gidajensu, da samar da agaji, da kuma fara aikin sake gina kasar."
Jami'in Hamas ya ce "Idan har sabon shirin ya kawo karshen ta'addancin da ake yi wa al'ummar Falasdinu da kuma janyewar sojojin mamaya, za mu mayar da martani mai kyau a kansa."
2000 GMT — Falasdinawa da dama sun shaƙe da hayaƙi mai sa hawaye da Isra'ila ta fesa a Nablus
Kamfanin dillancin labaran WAFA na kasar Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, Falasdinawa da dama sun shaƙe da hayaƙi mai sa hawaye da sojojin Isra'ila suka fesa a garin Beita da ke kudancin Nablus a Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
Rahoton ya ce sojoji sun harba bama-bamai da robobin iskar gas kan matasan yankin, lamarin da ya sa da dama daga cikinsu shaƙe da hayaƙi saboda shaƙar iskar gas.
1900 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 10 a hare-hare daban-daban da ta kai a Gaza
Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 10 tare da raunata wasu da dama ciki har da yara ƙanana, bayan da ta kai hari a wurare da dama a Gaza da aka yi wa ƙawanya.
Majiyoyi sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na WAFA cewa an kashe mutane biyu a Khan Younis, hudu a sansanin Nuseirat, hudu kuma a unguwar Daraj.