Wannan ne karon farko da aka soma shiga da kayayyakin agajin cikin Gaza tun bayan da aka soma wannan yakin. Hoto/Reuters

1420 GMT — Kusan mutum 100,000 sun fito zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a birnin Landan

Akalla mutum 100,000 suka fito zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a tsakiyar birnin Landan a yau Asabar inda suke neman Isra’ila ta tsagaita wuta kan hare-haren da take kai wa Gaza.

Wadanda suka fito zanga-zangar suna ta fadin kalaman “Free Palestine”, inda suke rike da alluna da kuma daga tutocin Falasdinu.

Masu zanga-zangar sun rinka yawo cikin Landan inda daga karshe suka taru baki daya a gaban gidan Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak. ‘Yan sanda sun yi kiyasin cewa akalla mutum 100, 000 suka shiga zanga-zangar.

1250 GMT — Isra'ila ta ce ba za ta amince a kai man fetur cikin Zirin Gaza ba

Mai magana da yawun sojin Isra’ila a ranar Asabar ya bayyana cewa Isra’ila ba za ta amince a kai man fetur cikin Zirin Gaza ba.

Ya bayyana cewa wannan yana daga cikin umarnin da shugabannin siyasa na Isra’ilar suka bayar.

“Muna kira ga mazauna arewacin Gaza da su tafi kudu, za a kai kayan agaji can, za mu ci gaba da luguden wuta a arewacin Zirin Gaza,” in ji Avichay Adraee.

Isra’ila ta hana shigar da fetur cikin Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba duk da gargadin da Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin kare hakkin bil adama suka yi.

0955 GMT — An kashe Falasdinawa sama da 350 a ranar Juma'a

Akalla Falasdinawa 352 aka kashe cikin kwana guda a Zirin Gaza a sa’o’i 24 da suka gabata, kamar yadda ofishin watsa labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana.

A wata sanarwa da shugaban ofishin Salama Maarouf ya fitar, hare-haren da Isra’ila ta kai a wurare da dama ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 352 a ranar da ta gabata.

A dayen bangaren, Ma’aikatar Lafiya ta Isra’ila a ranar Asabar ta bayyana cewa adadin wadanda suka samu rauni ya karu zuwa 5,007, daga ciki har da wadanda suke cikin matsanancin hali tun daga 7 ga watan Oktoba.

0855 GMT — An soma shiga da kayayyakin agaji Gaza daga Masar

Rukinin motocin farko dauke da kayayyakin agaji daga Masar sun soma shiga Gaza da aka yi wa kawanya ta iyakar Rafah, kamar yadda wani jami’in tsaro da kuma wani ma’aikacin kungiyar agaji ta Red Cross ta Masar suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Sama da manyan motoci 200 dauke da kusan tan 3,000 na kayayyakin agaji ne aka jibge a Rafah din tsawon kwanaki kafin suka soma shiga cikin Gaza.

Mutane da dama a Gaza sun koma cin abinci sau daya a rana ba tare da samun ruwan sha ba, inda suke tsananin jira domin kai musu kayan agaji.

Haka kuma ma’aikatan asibiti sun damu matuka sakamakon karancin kayayyakin kiwon lafiya da kuma man fetur da za a saka wa janareto domin samun wutar lantarki a asibitocin,

AA
AFP
AP
Reuters