Akalla shugabannin kasashen Afirka 25 ne suke birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu domin halartar taron kwanaki biyu da ƙasar ta shirya wanda aka soma daga ranar 4 ga Yuni zuwa 5 na watan Yuni, 2024. / Hoto: fadar gwmanatin Kenya   

Shugaba Yoon Suk Yeol na ƙasar Koriya ta Kudu ya sanar da ba da tallafi da zuba jarin biliyoyin daloli a kasashen Afirka, Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Koriya ta Kudu ke koƙarin bunƙasa huldar kasuwanci da nahiyar ta Afirka.

Birnin Seoul na karbar baƙuncin shugabannin kasashen Afirka 48 a wani babban taro da aka kaddamar a wannan makon, inda Yoon ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa, ƙasarsa za ta kulla yarjejeniya a dukkan abubuwan da suka shafi muhimman ma'adinai da ayyukan more rayuwa.

A yayin buɗe taron, Yoon ya yi alkawarin cewa gwmanatin Koriya ta Kudu za ta ruɓanya taimakon raya kasa da take bai wa Afirka zuwa dala biliyan 10 daga yanzu zuwa shekarar 2030, sannan kuma za ta samar da dala biliyan 14 na kuɗaɗen fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje don taimaka wa kamfanonin Koriya ta Kudu don su samu damar fadada kasuwanci da kuma zuba jari a nahiyar.

''Za kuma mu ba da tallafi sosai ga shirin yarjejeniyar 'yancin hadewar tattalin arzikin yankin Afirka (AfCFTA), wanda aka ƙaddamar a shekarar 2019,'' in ji Yoon.

Ƙarfafa Yarjejeniyar

An tsara shirin AfCFTA ne a matsayin yarjejeniyar 'yancin kasuwanci mafi girma a duniya ta fuskar yawan al'umma- inda aka tattara kasashe 54 daga cikin 55 na Afirka inda aka ware Eritrea ita kadai.

Kazalika Yoon ya sha alwashin "ƙarfafa yarjejeniyoyin" kan haɗin gwiwar kasuwanci da dama.

A yayin da Koriya ta Kudu ke koƙarin fadada ayyukan samar da ababen more rayuwa da haɗin gwiwar makamashi da kasashen Afirka, Yoon ya ce ƙasarsa wadda ke yankin gabashin Asiya tana sane tare da la'akari da tasirin sauyin yanayi a nahiyar.

Yayin da yake ba da misali da ayyuka irin su cibiyar samar da wutar lantarki ta Olkaria da ke kasar Kenya da kuma aikin gina tasarin adana makamashin batir a Afirka ta Kudu, '' Koriya za ta ci gaba da fadada ayyukanta tare da magance matsalar sauyin yanayi tare da kasashen Afirka,'' in ji Yoon.

'Ayyukan da za a iya aiwatarwa'

Tun da farko, Yoon ya shaida wa AFP cewa "akwai ɗimbin ayyuka masu inganci waɗanda Koriya ta Kudu da Afirka za su iya haɗa gwiwa domin aiwatarwa a dukkan fannonin samar da ababen more rayuwa."

Ayyukan sun hada da ''gina tituna da layin dogo da filayen tashi da saukar jiragen sama da tasoshin jiragen ruwa da samar da tsarin birane gami da sufurin zamani da kuma sauran manyan tsare-tsare,'' in ji shi.

An kaddamar da taron Koriya ta Kudu na kwanaki biyu, wanda aka soma daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Yunin 2024.

AFP