Musulmai a fadin duniya sun yi Babbar Sallah ko Sallar Layya a ranar Laraba, bayan da aka hau Arafa ranar Talata a Saudiyya.
A Kanada, wani mamba na Gundumar Majalisar Dokoku ta Mississauga Sheref Sabawy ya halarci Sallar Idi a Masallacin Anatolia da ke yankin Mississauga a Toronto, Canada.
A birnin Gaza na Falasdinu kuwa, ga wasu yara nan sun cancada ado suna yawon sallah.
Idan ba ka yi ba ni waje. Wani bajimi ne ya tsinke daga jikin igiyar da aka daura masa a yankin Etimesgut na birnin Ankara a Turkiyya.
Hakan ya sa duk jama'a suka yi ta kansu a kasuwar, da kyar aka kamo shi bayan da wata mota ta buge shi.
Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al Thani na uku daga dama, yana gabatar da Sallar Idi a Masallacin Lusail na kasar.
Wani rago ne ya yi zuru a hannun wanda ya saye shi a ranar sallah da safe a kasuwar sayar da dabbobi ta Naryn da ke kasar Kyrgyzstan.
A can birnin Landan na kasar Birtaniya kuwa, Musulmai ne suke ta taya juna murnar yin sallah lafiya bayan kammala sallar idi a Dandalin Highbury.
Yawon sallah, barka da sallah. Wasu 'yan yara a Nijeriya sun yi kwalliyarsu ta sallah bayan sauka daga Idi.
Mata ma aba a bar su a baya ba, inda suka halarci Sallar Idi a wata cibiyar gwamnati ta Bangsamoro a kasar Philippines.
Musulmai mata a Cibiyar Al'adu ta Muhammad Asad da ke Birnin Lviv na Ukraine.