Majalisar ministocin Isra'ila sun yi taro a birnin Tel Aviv a ranar Lahadi don tattaunawa kan matakin mayar da martani ga Tehran. / Hoto: AA  

An samu rabuwar kawuna tsakanin mambobin majalisar ministocin Isra'ila kan ma'auni da kuma lokacin da ya kamata a kai wa Iran hari.

Bayan harin ramuwar gayya da Iran ta kai wa Isra'ila a ranar Asabar da ba a taba ganin irinsa ba, an samu mabambantan ra'ayoyi a yayin taron majalisar ministocin Isra'ila da aka gudanar a ranar Lahadi a hedikwatar ma'aikatar tsaro da ke Tel Aviv, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana.

''Akwai yarjejeniya kan wajibcin mayar da martani kan harin Iran, amma an samu rarrabuwar kawuna da ya shafi ma'auni da kuma lokacin da za a mayar da martani, ba tare da an bijire wa matsin lambar Amurka da na kasashen duniya ba," kamar yadda Tashar talabijin ta Isra'ila 12 ta ruwaito.

A safiyar ranar Lahadin da ta wuce ne, gidan yada labarai na Isra’ila KAN ya fitar da sanarwar cewa ''cikin mintunan karshe ne aka soke matakin mayar da martani kan harin da Iran ta kai'' bayan wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da shugaban Amurka Joe Biden.

Sanarwar ta ba da shawara kan cewa "har yanzu ka'idojin tsaro na Isra'ila suna goyon bayan mayar da martani ga harin Iran, amma ba lallai ba ne a dauki mataki cikin gaggawa."

'Za mu dauki matakin da ya dace kan Iran idan lokaci ya yi'

Tashar talabijin ta Isra'ila 12 ta ba da rahoton cewa wasu daga cikin mambobin majalisar ministocin kasar Benny Gantz da Gadi Eisenkot sun ba da shawarar ''a mayar da martani ga harin a ranar Asabar, amma aka yi watsi da bukatarsu."

Kafar watsa shirye-shiryen ta yi nuni da cewa "wasu daga cikin ministocin sun ba da amincewarsu kan a yi kare-jini-biri-jini cikin ƙankanin lokaci kuma nan-take wato (fito na fito), yayin da wasu ke ganin gara a jira a kuma yi shiri a tsanake domin dole ne a mayar da martani mai karfi."

Majalisar ministocin ta yi wani taro a ranar Lahadi a hedkwatar ma'aikatar tsaro Isra'ila da ke Tel Aviv domin tattauna wa kan martanin da za a mayar wa Iran.

Majalisar tsaron ta bai wa Netanyahu da Ministan Tsaro Yoav Gallant da Gantz izinin sanin yadda Isra'ila za ta mayar da martani kan harin da Iran ta kai, wanda ke matsayin ramuwar gayya kan harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus na kasar Syria a ranar 1 ga watan Afrilu wanda ya yi sanadin mutuwar zaratan sojojin Iran bakwai. (IRGC), ciki har da janar biyu.

A sanarwar da aka fitar ta kafar Telebiji, Gantz ya bayyana cewa "za mu dauki matakin da ya dace kan Iran idan lokaci ya yi."

TRT World