Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a kullum waɗanda akasarinsu mata ne da yara. / Hoto: AFP / Photo: AA

1419 GMT — Wani jami’in Hamas ya ce masu shiga tsakani na kasa da kasa sun koma tattaunawa don cim ma yarjejeniya tsakanin kungiyar da Isra’ila kan tsagaita wuta a Gaza na Falasdinu.

Jami'in ya bayyana fatan ganin an cim ma yarjejeniyar kawo karshen yakin da Isra'ila da aka kwashe watanni 14 ana yi.

1100 GMT — Adadin wadanda suka mutu a yakin Isra'ila a Gaza ya haura 44,610

Ma'aikatar Lafiya a Zirin Gaza ta Falasdinu ta ce akalla mutum 44,612 ne suka mutu a cikin kusan watanni 14 na yakin Isra'ila a yankin Falasdinu.

Adadin wadanda suka mutu ya hada da mutuwar mutane 32 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, a cewar ma'aikatar, wadda ta ce mutum 105,834 ne suka jikkata a Gaza tun bayan mamayar da Isra'ila ta kai bayan harin da kungiyar Hamas ta kai kan iyakar kasar a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

1159 GMT — Hamas ta yi Allah-wadai da harin bama-bamai da Isra'ila ta kai a asibitin Gaza

Kungiyar Hamas ta yi Allah wadai da harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wata unguwa da ke kusa da asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 24 tare da jikkata wasu da dama.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi kakkausar suka ga sojojin Isra'ila kan kutsen da suka yi a asibitin, inda aka tilasta wa ma'aikatan jinya da ma'aikatan jinya ficewa tare da tsare mutane da dama.

Kungiyar masu fafutukar kare hakkin bil'adama ta bayyana hare-haren da ake ci gaba da kai wa a matsayin "lalacewar muhimman ababen more rayuwa na Gaza, musamman asibitoci, a zaman wani bangare na yakin kisan kare dangi."

0617 GMT — Sojojin Isra'ila sun yi wa asibitin Kamal Adwan da ke Gaza ƙawanya

Rundunar Sojin Isra'ila ta yi wa asibitin Kamal Adwan da ke Beit Lahia a arewacin Gaza ƙawanya inda suke ci gaba da buɗe wuta tare da toshe duka hanyoyin da ke zuwa asibitin, kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya bayyana.

Motocin soji na tunkafrar asibitin inda suke tafe suna ɓarin wuta inda ake jin ɓarin wutar daga ko ina da ke makwabtaka da asibitin.

Isra'ila ta kaddamar da wani gagarumin farmaki ta kasa a arewacin Gaza tun ranar 5 ga watan Oktoba domin "hana" kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas sake haduwa.

0046 GMT Isra’ila ta ƙwace kadada 5,930 ta filaye a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

Isra’ila ta sanar da ƙwace kadada 5,930 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, inda ta ayyana wurin da ta ƙwace a matsayin mallakarta da zummar faɗaɗa matsugunan ‘yan kama wuri zauna.

Kamar yada kafar watsa labaran Isra’ila ta Channel 14 ta bayyana, hukumomin Isra’ila ƙarƙashin jagorancin ministan kuɗi Bezalel Smotrich ya sanar da wannan matakin a abin da ya kira ɗaya daga cikin faɗaɗa ƙasar mafi girma a tsawon shekaru.

TRT Afrika da abokan hulda