Amurka tana adawa da mamayar Isra'ila a Lebanon amma ta aike da ƙarin sojoji Gabas ta Tsakiya / Hoto: AFP / Photo: Reuters

Litinin, 30 ga watan Satumba, 2024

1544 GMT — Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira da a kawo karshen duk wani tashin hankali a daidai lokacin da Isra'ila ke shirye-shiryen abin da ta kira "iyakance" mamaya a Lebanon a cikin fargabar barkewar yakin yankin.

Da wani dan jarida ya tambaye shi ko yana sane kuma yana jin dadin yadda Isra'ila ta fara kai hare-hare, Biden ya ce: "Na fi ku sanin abin da ke faruwa, kuma na ji dadin dakatawar su. Ya kamata mu tsagaita wuta a yanzu."

1428 GMT — Isra'ila ta sanar da Amurka game da shirinta na mamaye Lebanon - rahoto

Isra'ila na shirin "iyakance" hare-haren ƙasa a Lebanon wanda zai iya farawa nan da nan, kamar yadda ƙasar ta faɗa wa Amurka, in ji jaridar Washington Post tana ambato wani jami'in Amurka da ba a tantance ba.

Harin dai ba zai kai girman yakin da Isra'ila ta yi da kungiyar Hezbollah a shekarar 2006 ba, kuma zai mayar da hankali kan tsaro ga al'ummomin kan iyaka, in ji jami'in.

1002GMT Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a Gaza, adadin wadanda suka mutu ya haura 41,615

Yawan mutanen da suka mutu a yakin da Isra’ila ta yi a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba ya karu zuwa 41,615, in ji Ma’aikatar Lafiya a yankin da aka yi wa ƙawanya.

1236 GMT — Sojojin Lebanon sun ce an kashe wani soja a harin da Isra'ila ta kai ƙasarsu

Rundunar sojin Lebanon ta ce wani soja ya mutu a wani harin da Isra'ila ta kai kan wani babur a wani shingen binciken sojoji a kudancin Lebanon da ke kusa da kan iyaka.

Sanarwar da aka wallafa a shafin X ta ce, "An kashe wani soja a lokacin da wani jirgin sama mara matuki mallakar makiya Isra'ila ya kai hari kan wani babur a lokacin da yake wucewa ta shingen binciken sojojin Lebanon" a yankin Wazzani da ke kusa da kan iyakar Isra'ila".

Wannan dai shi ne soja na farko da aka sanar da kashe shi tun bayan da Isra'ila ta fara kai hare-haren bama-bamai a Labanon a makon jiya.

0822 GMT Mutum fiye da 100,000 sun tsere daga Lebanon zuwa Syria: MDD

Mutum fiye da 100,000 sun tsere daga Lebanon zuwa Syria tun da rikici ya yi ƙamari tsakanin Isra'ila da Hezbollah a watan nan, a cewar shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

Filippo Grandi ya wallafa saƙo a shafinsa na X cewa waɗanda suke tserewa sun haɗa da 'yan Lebanon da ’yan ƙasar Syria. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya tana taimaka wa mutanen da suka isa Syria, in ji shi.

0644 GMT — Isra'ila ta kashe shugabanni uku na Falasɗinawa a harin da ta kai tsakiyar Beirut

Dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare ta sama da sanyin safiyar Litinin a yankin Kola na birnin Beirut, wanda ya kasance irinsa na farko da suka kai a cikin babban birnin na Lebanon tun da suka soma yaƙi da Hezbollah a watan Oktoban da ya wuce.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito cewa jirgi mara matuƙi na Isra'ila ya kai hari a hawa na biyar na wani gida a kan hanyar da ta haɗa Beirut da Filin Jirin Saman Ƙasa da Ƙasa na Rafik Hariri.

Harin ya tayar da gobara a gidan, ko da yake 'yan kwana-kwana sun kashe ta.

Daga bisani ƙungiyar Popular Front for the Liberation of Palestine (PFLP) ta tabbatar da cewa harin ya kashe shugabanninta uku: Mohammed Abdel Aal, wani mamba na ɓangaren siyasarta kuma shugaban sashen soja da tsaro; Imad Ouda, kwamanda soji na Lebanon, da Abdel Rahman Abdel Aal, wanda ba a bayyana matsayinsa ba.

Ma'aikatan kwana-kwana suna ƙoƙarin kashe gobarar da ta tashi bayan Isra'ila ta kai hari a wani gidan bene a yankin Kola na birnin Beirut, ranar 30 ga watan Satumba, 2024. / Hoto: AA

0554 GMT Hamas ta tabbatar da kisan shugabanta a harin Isra'ila

Ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa, Hamas, ta ce an kashe shugabanta na Lebanon Fateh Sherif Abu el-Amin tare da iyalansa a wani hari da Isra'ila ta kai a kudancin ƙasar.

TRT Afrika da abokan hulda