1536 GMT — Amurka ta ƙi amincewa da ƙudurin MDD kan tsagaita wuta a Gaza a karo na uku
Amurka ta sake yin fatali da ƙudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya buƙaci a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza, duk da cewa Shugaba Joe Biden ya fuskanci matsin lamba na janye goyon bayan Isra'ila.
Wannan dai shi ne karo na uku da Amurka ta kaɗa ƙuri'a tun bayan fara yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza.
"Ci gaba da kaɗa ƙuri'a a yau abin fata ne kuma rashin gaskiya... ba za mu iya goyon bayan wani ƙuduri da zai jefa tattaunawar cikin haɗari ba," in ji Jakadiyar Washington a MDD Linda Thomas-Greenfield yayin da take ba da shawarar wani ƙuduri na daban da Amurka ta tsara.
1134 GMT — Shugaban Hamas Ismail Haniyeh ya isa Masar domin tattaunawa kan Gaza
Ƙungiyar Hamas a ranar Talata ta ce shugabanta Ismail Haniyeh ya isa birnin Alƙahira domin tattaunawa kan harin da Isra’ila ke kaiwa a Zirin Gaza.
A wata sanarwa da ƙungiyar Hamas ta fitar, ta ce Haniyeh da tawagarsa na shirin gudanar da tattaunawa da jami’an Masar kan batun siyasa da kuma halin da ake ciki a Gaza.
Haka kuma tattaunawar za ta mayar da hankali dangane da yadda za a dakatar da Isra’ila daga kai hare-hare a Gaza.
Zuwan Haniyeh na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an Qatar da Masar ke ci gaba da ƙoƙarin cimma yarjejeniyar musayar fursunoni da kuma tsagaita wuta.
0912 GMT — Hamas ta saka wa Isra'ila sharuɗɗa kan musayar fursunoni
Ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu ta ce za ta amince da yarjejeniyar musayar fursunoni da Isra’ila ne kaɗai idan Isra’ilar ta amince da cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma shigar da kayayyakin agaji Gaza.
“Mayar da fursunonin Isra’ila na ɗauke da sharuɗɗa uku. Na farko shi ne samun sauƙin mutanenmu da komawarsu rayuwarsu ta asali. Na biyu shi ne kawo ƙarshen zalunci na uku shi ne musayar fursunoni na asali wanda za a fito da mutanenmu 10,000 da ke cikin gidajen yarin Isra’ila,” in ji Khalil al Hayya, wanda mamba ne a Hamas a yayin wata tattaunawarsa da kafar watsa labarai ta Al Jazeera.
0753 GMT — Isra'ila ta sanar da mutuwar wani sojanta da aka raunata a Khan Younis
Rundunar Sojin Isra’ila ta sanar da mutuwar ƙarin sojinta ɗaya wanda ya samu rauni a yayin wata arangama da Falasɗinwa a kudancin Zirin Gaza.
A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta bayyana cewa sojan da ya mutu Staff Sgt. Maoz Morell mai shekara 22, ya samu mummunan rauni a ranar 15 ga watan Fabrarairu a yayin wata arangama da Falasɗinawa wadda ta yi sanadin mutuwar sojin Isra’ila ɗaya da raunata takwas.
Aƙalla sojojin Isra’ila 236 aka kashe a Gaza tun bayan da Isra’ila ta soma kai hari ta ƙasa a Gaza a ranar 27 ga watan Oktoba, sai dai jimlar adadin sojin da aka kashe tun bayan soma rikicin a ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 575.