Sukar ta Celik na zuwa ne bayan da aka sanya haramci da dokoki na gudanar da jerin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Turai. Hoto: TRT World

Matsin lambar da gwamnatocin Ƙasashen Yamma ke nunawa don hana jerin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu da ake yi a fadin duniya da kuma yadda suke nuna cewa duk wani goyon baya da za a nuna wa Falasdinawa laifi ne, abu ne da ba za a yarda da shi ba, a cewar mai magana da yawun Jam'iyyar AK ta Turkiyya a ranar Litinin.

"Matakan da dakarun tsaron Isra'ila ke ɗauka a kan mutanen Gaza abubuwa ne na take hakkin darajojin ɗan'adam da ƴancin dan'adam da kuma dokokin ƙasa da ƙasa," a cewar Omer Celik, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban Jam'iyyar ta AK Party.

"Mutane a faɗin duniya suna da duk wata dama ta mayar da martani a kan wannan lamari."

Sukar ta Celik na zuwa ne bayan da aka sanya haramci da dokoki na gudanar da jerin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Turai, lamarin da ya jawo damuwa da kan batun ƴancin fadin albarkacin baki da taruka.

"Sun yi ƙoƙarin haramta duk wata zanga-zangar goyon bayan Falasɗiwa. Duk masu ƙoƙarin haramta waɗannan zanga-zanga don son zuciyarsu to suna goyon bayan mulkin zalinci ne," in ji Celik.

"A wasu ƙasashen Yamma da dama, ana matsa lamba kan masu gudanar da jerin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a wuraren taruwar jama'a da jami'o'i ne a wani yunƙuri na rufe gazawar ƙasashen," ya ce.

"Duk masu nuna son rai a kan yin adalci, ciki har da kisan yara ƙanana, to fa ba su da bakin magana kuma a kan adalci," ya faɗa.

Faransa da Birtaniya da Jamus da Netherlands su ne ƙasashen Turan da suke ƙoƙarin ganin an haramta yin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu, inda har hukumomin Faransa suke haramta amfani da tutocin Falasɗinu.

Rikicin da ake yi

Dakarun Isra’ila sun ƙaddamar da wasu hare-haren soji a kan Gaza bayan da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu ta kai wasu hare-haren ba-zata yankunan Isra’ilan.

Rikicin ya fara ne bayan da Hamas ta ƙaddamar da shirin Operation Al Aqsa Flood – wasu jerin hare-haren ban mamaki da suka haɗa da harba rokoki cikin Isra’ila ta sama da ta ƙasa da ta ruwa.

Hamas ta ce ta kai hare-haren ne a matsayin martani kan yawan afkawa Masallacin Ƙudus da sojojin Isra’ila ke yawan yi a Gabashin Birnin Ƙudus da kuma yadda Yahudawa ‘yan kama wuri zauna suke ƙara uzzurawa Falasɗinawa.

Rundunar sojin Isra’ila ta ƙaddamar da shirin Operation Swords na kai wa yankunan Hamas hare-hare a Gaza a matsayin martani.

Wannan martanin ne ya ci gaba har Isra’ila ta yanke wa Gaza ruwa da wuta, lamarin da ya ta’azzara yanayin da ake ciki a yankin.

TRT World