1057 GMT — Akalla Falasdinawa 44,363 ne aka kashe tare da jikkata 105,070 a farmakin da sojojin Isra'ila suka kai a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba, 2023, in ji ma'aikatar lafiya ta Gaza.
1151 GMT — Tankunan yaki na Isra'ila sun shiga kauyen kan iyakar Lebanon
Tankokin yaki 4 na Isra'ila sun shiga yammacin kauyen Khyam na kan iyakar kasar Lebanon, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Labanon ya sanar, bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar Laraba.
1137 GMT — Mutum 30 ne suka mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai a tsakiyar sansanin Gaza: likitoci
Harin da sojojin Isra'ila suka kai cikin dare ya kashe Falasdinawa akalla 30 a cikin dare a Gaza, yawancinsu a sansanin Nuseirat da ke tsakiyar yankin, in ji likitoci, bayan da wasu tankokin yaki suka ja da baya daga wani yanki da suka kai farmaki.
Likitoci sun ce sun gano gawarwakin Falasdinawa 19 da aka kashe a yankunan arewacin Nuseirat, daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira takwas da ke yankin.
Likitocin sun kara da cewa an kashe sauran a yankunan arewaci da kudancin Gaza.
Wasu tankunan yaki na Isra'ila sun ci gaba da aiki a yankin yammacin sansanin kuma Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Falasdinu ta ce tawagogin sun kasa amsa kiraye-kirayen neman agaji daga mazauna cikin gidajensu.
0435 GMT — Harin Isra'ila ya kashe ƙarin Falasɗinawa 8 a Gaza
Sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla takwas, daga ciki har da biyar waɗanda 'yan gida ɗaya ne a wasu jerin hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a faɗin Gaza.
A wani hari da aka kai a sansanin gudun hijira na Nuseirat, mutum biyar ne suka rasa rayukansu.
Hukumomin Isra'ila sun bayar da rahoton cewa akwai wasu mutum uku da suka rasu a wani hari na daban da Isra'ilar ta kai yammacin birnin Gaza.