Akalla mutum 111 ne suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta yi sanadiyar ruguje wasu gine-gine a arewa maso yammacin China, kamar yadda kafafen watsa labarai na kasar suka rawaito.
Tuni dai masu aikin ceto suka bazama tono ɓaraguzan gine-gine don gano waɗanda suke ƙarƙashi.
A cewar gidan talabijin na CCTV, mutum 11 sun mutu yayin da mutum 100 suka jikkata a birnin Haidong da ke maƙwabtaka da lardin Qinghai.
Girgizar kasar ta haifar da ɓarna sosai ciki har da rusa gidaje, tare da sanya mutane tsarewa zuwa kan tituna don neman tsira, a cewar kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
An soma aikin ceto da sanyin safiyar ranar Talata, inda shugaban kasar Xi Jinping ya yi kira da a a hada kai wajen ''aikin gayya'' don ceto wadanda suka tsira da dukiyoyinsu.
Girgizar kasar wanda ƙarfinta ya kai maki 5.9 kamar yadda hukumar binciken yanayin kasa ta Amurka ta bayyana, ta afku ne a yankin Gansu da ke kusa da iyakar Qinghai, inda lardin Haidong yake.
Wurin da girgizar kasar ta auku ya kai tazarar kilomita 100 daga kudu maso yamma da babban birnin lardin Gansu, Lanzhou.
Bayan babbar girgizar kasar ta farko an yi ta samun wasu ƙanana da suka biyo baya.
Kafar Xinhua ta rawaito cewa saboda ƙarfin girgizar kasar mai maki 6.2 - sai da aka jiyo ta a yankin Xian na arewacin lardin Shaanxi, mai nisan tazarar kilomita 570.
Tsananin yanayin hunturu
Wutar lantarki da hanyoyin samun ruwa sun katse a wasu ƙauyuka da ke yankin, a cewar kafar Xinhua.
Gidan talabijin na CCTV ya nuna bidiyon wasu motocin gaggawa da ke tuƙi zuwa wurin da lamarin ya faru inda suka haska fitulunsu kan manyan titunan da dusar kankara ta lullube.
An dauki hoton masu aikin ceto sanye da rigar sanyi kafada-da-kafada a cikin manyan motocinsu, yayin da wasu hotuna suka nuna sun yi jerin gwano domin karɓar umarni.
Yanayin sanyi ya yi tsanani a fadin arewacin China, wasu faifan bidiyon CCTV daga daya daga cikin wuraren da lamarin ya fi kamari ya nuna yadda mazauna ke dumama kansu da wuta yayin da jami'an agajin gaggawa ke kokarin kafa tantuna.
Girgizar kasar mai zurfin kilomita goma ya auku ne da misalin 11:59 na dare agogon kasar wato karfe (15: 59 GMT) na ranar Litinin, a cewar hukumar kula da yanayin kasa ta USGS wacce ta yi bitar girman makin bayan rahoton da bayar na maki 6.0.
Jami'an kasar sun kaddamar da aikin agajin gaggawa tare da tura jami'an ceto zuwa yankin bayan faruwar lamarin, a cewar rahoton Xinhua.
Girgizar kasa ba sabon abu ba ne a China, ko a watan Agusta an fuskanci girgizar kasa mai karfin maki 5.4 a yankin gabashin kasar, inda mutum 23 suka jikkata, tare da rushe gine-gine da dama.
Kazalika a watan Satumban shekarar 2022, girgizar kasa mai karfin maki 6.6 ta afku a lardin Sichuan inda kusan 100 suka mutu.
Sannan a shekarar 2008 an yi wata girgizar kasa mai karfin maki 7.9 da ya yi sanadiyar mutuwar mutum fiye da 87,000 ko kuma suka bata, ciki har da daliban makaranta mutum 5,335.