Litinin, 9 ga Satumban 2024
1346 GMT –– Akalla wasu Falasdinawa 16 aka kashe a hare-haren Isra’ila a Gaza, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu tun daga ranar 7 ga watan Oktoba zuwa 40,988, in ji ma’aikatar lafiya a yankin da yaki ya daidaita.
Sanarwar ma'aikatar ta kara da cewa wasu mutane 94,825 sun samu raunuka a harin.
"Sojojin Isra'ila sun kashe mutane 16 tare da raunata wasu 64 a wasu 'kisan gilla' biyu da suka yi wa wasu iyalai a cikin sa'o'i 24 da suka gabata," in ji ma'aikatar.
1145 GMT –– An yi jana'izar Baturkiyya-Ba'amurkiya 'yar gwagwarmaya da aka kashe a Gabar Yammacin Kogin Jodan
Ɗaruruwan Falasɗinawa a birnin Nablus da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan sun yi jana’izar Baturkiya Ba’amurkiya ‘yar gwagwaryma Aysenur Ezgi Eygi wadda sojojin Isra’ila suka harbe a ranar Juma’a.
Ɗumbin mutane sun raka gawarta tun daga asibitin gwamnati na Rafidia da ke Nablus inda suka ratsa tituna da dama na ƙasar inda suka rinƙa Allah wadai da zaluncin da Isra’ila ke yi tare da jinjina wa ƙasashen da ke taimaka musu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito.
Masu makoki sun gudanar da sallar jana'izar, karkashin jagorancin gwamnan Nablus Ghassan Daghlas, tare da halartar shugabanni daga bangarori daban-daban na Falasdinu da kuma dimbin jama'a.
1011 GMT –– Hare-haren Isra'il a Gaɓar Yamma sun ta'azzara al'amura - MDD
Manyan ayyukan soja da da Isra'ila ke yi a Gaɓar Yamma da aka mamaye suna mummunan ta'azzara al'amura a yankin da dama tuni yake ciki "mawuyacin" yanayi, wanda ya ƙara ta'azzara irin ta'annatin da 'yan kama-wuri-zauna ke yi, a cewar babban jami'in kare haƙƙin ɗan adam na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
Da yake buɗe wani taro na Hukumar Kula da Haƙƙin Dan Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Geneva, Volker Turk ya koka kan yadda ake ƙara aikata ta'annati a Gaɓar Yamma, a lokacin da Isra'ila ke ci gaba da kai manyan hare-hare.
"A Gaɓar Yamma, mummunan ayyukan da ake yi, wasu a wani irin mataki da ba a taɓa gainin irinsa ba a cikin shekaru 20, suna ta'azzara yanayin da ake ciki, wanda dama tuni ya taɓarɓare, saboda ta'annatin da 'yan kam-wuri-zauna suke yi, kamar yadda Turk ya shaida wa Majalisar.
0125 GMT — Isra'ila ta kutsa kai cikin sansanonin Falasdinawa, inda rikici ya ɓarke da mazauna yankin
Sojojin Isra'ila sun kai farmaki a garin Tulkarem da sansanin 'yan gudun hijira na Balata da ke arewacin Gabar Yammacin Kogin Jordan.
Dakarun mamaya na Isra'ila sun mamaye Tulkarem bayan tsakar dare, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasdinawa Wafa ya bayyana.
Rahoton ya kara da cewa, wasu motocin sojojin mamaya tare da rakiyar manyan buldoza guda biyu sun shiga birnin daga bangarensa na yammacin kasar, inda suka fara rusa ababen more rayuwa a yankin Al-Alemi, yayin da wani jirgin sama mara matuki na sa ido ya yi ta shawagi ta saman birnin.
Wafa ya kuma ruwaito cewa, sojojin Isra'ila sun kai farmaki sansanin 'yan gudun hijira na Balata da ke gabashin Nablus tare da rakiyar buldoza ta soji, lamarin da ya kai ga arangama da dakarun gwagwarmayar Falasdinawa.
Shaidun gani da ido sun ce an yi arangama tsakanin Falasdinawa da sojoji a kofar shiga sansanin.
Masu fafutuka sun yada bidiyon da ke nuna motocin soji da kuma buldoza yayin farmakin.
0136 GMT — Majalisar ministocin tsaron Isra'ila ta yi taro don magance tashe-tashen hankula a Gabar Yammacin Kogin Jordan
Ma'aikatar tsaron Isra'ila karkashin jagorancin Firaminista Benjamin Netanyahu, ta yi taro domin tattauna muhimman batutuwa da dama, musamman tabarbarewar yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye, kamar yadda hukumar yada labaran kasar ta sanar.
Hukumar ta yi nuni da cewa Netanyahu ya bude zaman, inda aka tattauna batutuwa da dama, tare da mai da hankali kan yadda al'amura ke kara tabarbarewa a yankin Falasdinu da aka mamaye.
Yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a Gaza, sojojin Isra'ila sun fadada ayyukansu tare da kara kai hare-hare a Yammacin Gabar Kogin Jordan da suka mamaye, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 692 tare da jikkata wasu kimanin 5,700, baya ga wadanda aka kama a cewar majiyoyin hukumomin Falasdinu.
A yayin ganawar, Netanyahu ya kuma tabo ziyarar da ministocin gwamnati ke yawan kaiwa Masallacin Ƙudus.