1727 GMT — Adadin Falasɗinawa da suka mutu ya kai 35,857 a lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a Gaza tun daga 7 ga Oktoban bara, a cewar Ma’aikatar Lafiya a yankin da aka mamaye.
An jikkata aƙalla mutane 80,293 a hare-haren da Isra’ila ke kai wa, kamar yadda ma’aikatar ta faɗa a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a.
0311 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 10 a sabbin hare-hare da ta kai Gaza
Sojojin Isra'ila sun kai hari a wani gida da ke Birnin Gaza, inda suka kashe Falasɗinawa 10 tare da jikkata wasu da dama, a cewar kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu, WAFA.
Majiyoyi a yankin sun shaida wa WAFA cewa dakarun Isra'ila sun kai hari a gidan iyalan wani Bafalasɗine mai suna Ayoub a yankin Al-Sha'abiyah na birnin, inda suka kashe Falasɗinawa 10, ciki har da yara da mata.
Kazalika sun jikkata mutane da yawa.
0100 GMT — Netanyahu zai yi jawabi ga 'yan majalisar dokokin Amurka 'nan ba da jimawa ba'
Nan ba da jimawa ba ne Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai gabatar da jawabi ga 'yan majalisar dokokin Amurka, a cewar kakakin majalisar wakilan ƙasar Mike Johnson, a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza.
"Nan ba da daɗewa ba ne za mu karɓi baƙuncin Firaminista Netanyahu a zaman haɗin-gwiwa na Majalisar Dokokin Amurka," in ji Johnson, inda ya ƙara da cewa ziyarar tasa za ta nuna "gagarumin goyon bayan da muke bai wa gwamnatin Isra'ila."