Wani sojan Indiya yayin da yake duba wani gida da wasu gungun matasa suka kona a wani yanki da yake yawan fama da rikicin kabilanci a kauyen Heiroklian a gundumar Senapati a jihar Manipur /Hoto: AFP

Rikice-rikecen kabilanci da tarzoma sun yi sanadiyyar mutuwar mutum a kalla 60 wasu kuma fiye da 35,000 sun rasa muhallinsu a cikin 'yan kwanakin nan a Manipur, wata karamar jiha da ke Arewa-maso-gabashin kasar Indiya.

Dole ta sa mahukunta neman taimako daga sojoji saboda a kashe wutar rikicin da kuma "ba su umarnin harbin" duk wanda suka ga yana kokarin tada zaune tsaye a kewayen tsaunin Imphal, wurin da galibin mazauna jihar miliyan 2.5 suke zaune.

An katse intanet a wani kokari da mahukunta suke na takaita yaduwar labaran karya, yayin da jami'an tsaro suke sintiri ta sama da jirgi mai saukar ungulu da kuma jirage marasa matuka.

Dubban mutane daga al'ummar Meitei ciki har da kabilun Kukis da Nagas, dole suka koma wasu wurare na wucin-gadi wadanda gwamnati ta samar.

Meiteis, wadanda mabiya addinin Hindu ne, su ne kashi 60 cikin 100 na jama'ar jihar. Su kuma kabilar Kukis da Nagas yawancinsu Kiristoci ne.

Yadda rikicin ya samo asali

Jihar Manipur tana da tarihin rikicin kabilanci wanda ya kara kamari saboda iyakar da jihar ta yi da kasar Myanmar.

A makon jiya, rikici ya barke biyo bayan wata zanga-zanga da kabilar Kuki ta yi, inda take nuna rashin gamsuwarta ga daukaka matsayin wata kabilar jihar.

Al'ummar Meitie ta dade tana neman a saka ta a wani jerin da ake kira Scheduled Tribe Category, wanda hakan zai ba ta damar amfani da dazuka da samun ayyukan gwamnati da kuma ilimi.

Amma kabilun da ke cikin wannan jerin musamman Kukis wadanda suke zaune a tsaunuka, suna tsoron ka da a kwace musu ikon da suke da shi a kan dazukan da suka gada daga iyaye da kakanni, idan aka amince da bukatar Meitei.

Indiya tana kebe wasu ayyukan gwamnati da guraben karatu da kujerun masalisa ga kabilun da ke cikin jerin Scheduled Tribes don tafiya da su da kuma damawa da kowa da kowa.

Kabilun da ke jerin Scheduled Castes (SCs) da na Scheduled Tribes (STs) su ne kabilun da a hukumance a Indiya ake ganin ba a damawa da su.

Lokacin mulkin mallakar Birtaniya, ana kiransu da kabilun Depressed Classes.

Bayan samun 'yancin kan Indiya, kabilun da ke jerin Scheduled Castes da Scheduled Tribes an ba su wani matsayi da za a rika ba su fifiko, wanda hakan yake tabbar musu da wakilcinsu a siyasance da ware musu wasu guraben karatu da ayyukan gwamnati.

Tarihin rikicin

Za a iya alakanta rikicin da ke faruwa a Manipur da batun mallakar kasa da kuma batun yadda ake nuna wasu fifiko, wadannan dalilai ne suka rika jawo rikici tsakanin kabilu a jihar.

Manipur yanki ne da ke Arewa-maso-gabashin Indiya da yake da mabambantar al'ummomi kamar Meiteis da Kikis da kuma Nagas wadanda suke da dadadden tarihin rashin yarda da juna.

Kashi 60 cikin 100 na Meiteis mabiya addinin Hindu ne, amma kuma suna da wadanda suke bin addinin iyaye da kakanni a cikinsu.

A cikin kabiar Meitei, akwai Musulmi wadanda su ne kaso takwas cikin 100.

A baya an rika samun rikicin addini tsakanin 'yan kabilar Meitei Musulmai da mabiya addinin Hindu. 'Yan kabilar Meiteis sun fi masu karatu da samun wakilci a fannin kasuwanci da siyasa idan aka kwatanta da Kukis da Nagas.

Al'ummomin sun hada da Kukis da Nagas wadanda su ne kaso 30 cikin 100 na al'ummomin da ke rayuwa a kan tsauni.

Galibin Kukis da Nagas da ke Manipur suna bin addinin Kirista ne, sai dai Kukis sun warwatsu a yankin Arewa-maso-gabashin Indiya da Myanmar.

Galibin Kukis sun hijira ne daga Myanmar zuwa Indiya inda a farko shugabannin Meitei suka tsugunar da su a tsaunuka don su taimaka wajen kare Meitei daga Nagas, wadanda suke kai hare-hare tsaunuka.

Lokacin ayyukan ta da kayar baya a Nagaland, Naga sun yi ikirarin cewa Kukis sun mamaye wurare don su balle su kafa jiharsu ta Naga.

An samu tashe-tashen hankula a shekarar 1993 tsakanin Nagas da Kukis a Manipur, inda Nagas suka kashe rayuka fiye da 100.

Duk da tarihin tashin hankali tsakaninsu, Nagas da Kukis sukan hada kansu don su yakar Meitei saboda suna adawa da bukatarsu ta shiga jerin kabilun "Scheduled Tribe".

TRT World