Saudiyya ta soma bayar da bizar Umrah ta sabuwar shekarar Musulunci

Saudiyya ta soma bayar da bizar Umrah ta sabuwar shekarar Musulunci

Ma'aikatar Aikin Hajji da Umrah ta sanar da hanyar da za a bi domin samun bizar tafiya Aikin Umrah.
Ana dakatar da zuwa Umrah ne da zarar Aikin Hajji ya matso, sa'annan a ci gaba bayan Aikin Hajji. Hoto/AA

Ma’aikatar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta soma bayar da bizar tafiya Umrah ta intanet a sabuwar shekarar Musulunci.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan kammala Aikin Hajjin bana inda tuni wasu daga cikin Alhazai suka soma komawa kasashensu.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito ma’aikatar inda take cewa masu son zuwa Umrah za su iya neman biza din ta hanyar cike fom a wannan shafin na Nusuk: https://www.nusuk.sa/ar/about .

Ma'aikatar ta kuma ce masu son zuwa Umrah za su soma zuwa kasar daga ranar 19 ga watan Yulin 2023, wanda ya yi daidai da 1 ga watan Muharram na shekarar 1445.

Ma’aikatar ta ce a shafin ne mai son yin Umrah zai samu gidan da yake so ko otel da motar sufuri da sauran bukatu.

Sabbin tsare-tsaren da aka fito da su a halin yanzu da gwamnatin kasar ta fito da su sun bayar da dama ga mata su iya zuwa Umrah ba tare da muharrami ba.

TRT Afrika da abokan hulda