Ofishin jakadancin China ya yi martani ne ga wani rahoto na jaridar The Times ta Birtaniya / Hoto: Reuters

Ofishin jakadancin China ya musanta zargin daukar nauyin ta’addanci a Nijeriya.

Kakakin ofishin jakadancin ne ya fitar da sanarwar da aka wallafa a shafinsu na intanet da kuma Twitter.

Sanarwar ta mayar da martani kan wani rahoto da jaridar The Times ta Birtaniya ta buga ranar 15 ga watan Afrilu, inda ta zargi ‘yan kasar China da biyan 'yan bindiga don samun damar diban ma’adanai a wasu yankunan Nijeriya.

Martanin kasar China ya mai da hankali kan kalaman jaridar cewa, “A kaikaice za a iya cewa Beijing tana daukar nauyin ta’addanci” a Nijeriya.

Ofishin jakadancin ya ce“an gina wannan labari ne kan bayanai da ba a tantance ba, masu rudani, kuma wadanda ba a tabbatar da sahihancinsu ba. Muna nuna matukar rashin jin dadinmu, da kuma watsi da shi”.

Sanarwar ta ce, “A kullum, gwamnatin China da ofishin jakadancin China a Nijeriya suna jaddada wa kamfanoninmu da ‘yan kasar da ke Nijeriya cewa su bi doka da tsare-tsaren Nijeriya.”

Ta kara da cewa, “Gwamnatin China ba za ta taba shiga harkar daukar nauyin ta’addanci ta kowace irin hanya ba. Zarge-zargen da ke cikin rahoton ba su da wata makama, kuma ba su dace da tsarin aikin jarida ba shi ya sa muke tuhumar manufarsa”.

A wancan rahoton da The Times ta wallafa, ta yi zargi cewa wasu ‘yan asalin China da ke aikin hakar ma’adanai ba bisa doka ba, suna aiki tare da ‘yan ta’addan da ke damun jihar Zamfara, da ma wasu yankuna da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Wannan zargi ya janyo muhawara kan matsalar tsaro a arewacin Nijeriya, da kuma alakar matsalar da ayyukan masu hakar ma’adanai kamar zinare, a yankuna da ake fama da hare-hare da kashe-kashe tsawon shekaru.

A yanzu dai, kasar China ta nesanta kanta daga duk wasu ayyukan da suka dangaci rashin tsaro da rikice-rikice a Nijeriya.

Kakakin ofishin jakadancin ya kuma ce, “China za ta ci gaba da tallafa wa yunkurin Nijeriya na gina kasa, da kuma kawo tsaro ga al’ummarta”.

Ya ce “Muna maraba da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, kuma muna watsi da duka wata manufa ko yunkuri na bata wannan hadin gwiwa.”

TRT Afrika