Jirgin saman Indiya PSLV-C23, dauke da tauraron dan adam biyar, ya tashi daga Cibiyar Sararin Samaniya ta Satish Dhawan a Sriharikota / Hoto: Reuters  

Indiya ta zama ƙasa ta huɗu cikin ƙasashen da suka taba sauka a kan duniyar wata, sannan ta farko wacce ta sauka a ƙuryar ɓangaren kudu na Duniyar Watan.

Ziyarar da jirgin sama jannati na Vikram Lander ya yi zuwa Duniyar Wata a shekarar nan ta 2023 ya sabunta rige-rigen da ƙasashe ke yi Duniyar Earth zuwa Wata, bayan irin wannan yunƙuri da Rasha da wani kamfanin kasar Japan mai zaman kansa suka yi na zuwa can.

Ana sa ran cikin shekarar 2024, hukumomin kula da kimiyyar sararin samaniya na kasashen China da Japan da wasu kamfanonin Amurka biyu su ma su sauka a sararin Duniyar Wata.

Ƙoƙarin na Indiya ya zo ne bayan wasu 'yan kwanaki da jirgin Luna- 25 na kasar Rasha wanda shi ma ya nufi yankin sararin Duniyar Watan ya faɗo, bayan yin hatsari.

Kwanaki kadan bayan saukar jirgin Indiya a Watan, kasar ta kuma kaddamar da wani aiki na nazari kan Sararin Duniyar Rana.

Cikin bakin ramin

A watan Yuli ne, hukumar kula da kimiyyar sararin samaniyar Amurka NASA ta ba da sanarwar cewa na'urarta da ke hangen nesa ta James Webb ta gano wani abu da ake kyautata zaton shi ne baƙin rami mafi girma da ke tsakiyar birnin taurari na CEERS 1019.

A cewar masu bincike, ramin ya samo asali tun kafin Babbar Fashewar ta Big Bang da ta faru, wajen kimanin shekara miliyan 570.

An kuma yi imanin cewa nauyin baƙin ramin ya zarce na Rana sau miliyan tara.

"Birnin taurari na CEERS 1019, ya samu ne sama da shekaru miliyan 570 bayan Babbar Fashewar da aka yi, sannan baƙin ramin bai kai sauran da aka gano ba a tun farkon samuwar sararin subhana,'' in ji bayanan da NASA ta fitar a shafinta na intanet.

NASA ta ƙara da cewa, masu bincike sun “gano” wasu ƙarin baƙaƙen ramuka guda biyu da suka ce suna “kan wani ƙaramin yanki, sannan sun wanzu ne shekaru biliyan daya zuwa 1.1 bayan Babbar Fashewar da aka samu.”

"Webb ya kuma gano biranen taurari 11 da suka wanzu a lokacin da sararin subhana ke da shekara miliyan 470 zuwa 675," in ji NASA.

Hukumar kula da kimiyyar sararin samaniya ta Amurka NASA ta ce baƙin ramin da ke birnin CEERS 1019 ya samo asali ne tun lokacin baya da "da kusan nauyin Rana sau miliyan tara, nesa da sauran baƙaƙen ramukan da suka wanzu a farkon samuwar sararin subhana da aka gano su da sauran na'urorin hangen nesa.''

A cewar NASA "girman ramin" zai iya ɗaukar kamar Rana fiye da biliyan daya sannan suna da sauƙin ganowa saboda sun ''fi haske.''

Zayyanar sararin subhana daga biranen taurari masu nisa

Kazalika ita ma Hukumar Kula da Kimiyyar Sararin Samaniya ta Turai (ESA) ta bayyana wasu hotunan farko na biranen taurari masu haske da na'urarta mai hangen nesa ta dauka daga nisan dubban shekarun haske.

Manufar na'urar hangen nesa ta ''Euclid Telescope'' ita ce ta hada taswira mafi girma ta sararin samaniya da fasahar 3D, ta yadda za a iya ganin sinadaran da ke yawo a samaniya na "dark matter" da "dark energy," tamkar yadda suke a zahiri, waɗanda masana kimiyya suka yi amannar cewa su ne suka mamaye kashi 95 na sararin subhana.

Har ila yau, na'urar hangen nesa ta ESA ta gano wani haske na "gamma rays" daga wata tauraruwa da masu bincike suka ce ta fashe daga nisan kusan shekarun haske biliyan biyu daga Duniyar Earth.

An kwatanta cewa hasken gamma-ray ko kuma ''GRB 221009A ya fi duk wani abu mai ƙarfi da aka taɓa lissafin irinsa a ba, yayin da hasken gamma-ray ke isowa duniya ne sau ɗaya kawai a duk shekara 10,000.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, karfin hasken GRB 221009A ya kai sau goma fiye da ko wane abu da aka taba lissafawa a baya, a kan samu saukar kwayar haske gamma-ray sau daya a cikin shekaru 10,000.

NASA ta samo wani guntun dutsen da ke shawagi a sararin samaniya

Hukumar Kula da Kimiyyar Sararin Samaniyar Amurka ta sanar da samun wasu samfura da aka tattaro daga dutsen astiriyod da ke shawagi a sararin subhana mai sun Bennu da ke yawo a kusa da Duniyar Earth.

Hukumar ta ce samfuran akwai ruwa da iskar carbon da kuma ma'adinan karfe a jikin dutsen da aka yi imanin cewa ya kai shekaru biliyan 4.5 na rayuwar da kumbon jirgin OSIRIS- REx ya yi a wajen.

Aikin, wanda aka shafe tsawon shekara bakwai ana yin sa, ya sa an yi nasarar tattaro giram 250 na ura da wayoyin halittu, ninki hudu fiye da yadda aka yi tsammani.

Hukumar ta NASA ta ce aikin ya shafe tafiyar kusan mil biliyan hudu a sararin Unguwar Rana zuwa Bennu, kafin a dawo duniyar Earth don samar da muhimman amsoshin tambayoyin da suka shafi rayuwa da asalin abubuwan da suka faru a sararin samaniya.

Masu zuwa yawon bude ido a sararin samaniya

Jirgin Virgin Galactic na ɗan kasuwan Birtaniya Richard Branson, ya soma daukar masu yawon bude ido zuwa sararin samaniya a tafiya mai gajeren zango bayan ƙaddamar da bulaguron da wasu mutum biyar suka yi a tsawon watanni da dama daga New Mexico.

An shirya tafiya da wasu mutane kadan nan gaba kafin kamfanin ya ɗan dakatar da tafiye-tafiyen a tsakiyar shekarar 2024 don haɓaka jirginsa na roka wanda zai iya tafiya da karin mutane akai-akai.

TRT World