Turkiyya tana fuskantar zabuka biyu a ranar 14 ga watan Mayu wadanda za su yi tasiri sosai ga makomar kasar.
A tsawon shekaru 20 da suka wuce jam'iyyar Justice and Development (AK) ta mamaye fagen siyasar kasar karkashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan, wanda yake mulkin kasar tun daga shekarar 2002.
An bayyana Recep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban kasar Turkiyya na farko mai cikakken iko a shekarar 2018, bayan wani muhimmin gyara da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar.
Turkiye tana bin salon mulkin majalisa ne tun farkon fara zabe da jam'iyyu da dama suka shiga a shekarar 1946, kuma a shekaru 20 da suka wuce, tun daga 2002 jam'iyya daya ce take mulkin kasar.
Jam'iyyar AK, karkashin mulkin Recep Tayyip Erdogan ta rika samun nasara a duka zabukan da aka yi.
Tsawon wadannan shekaru, Turkiyya ta samu gagarumin ci gaba a fannin kirkire-kirkire a ciki da wajen kasar.
Kasar ta rikida inda ta kawo kyakkyawan fata ga sauran duniya, musamman kananan kasashe wadanda manyan kasashe suke hana su rawan gaban hantsi.
A yanzu haka Turkiyya ce kasa ta 19 a girman tattalin arziki a duniya, a ma'unin tattalin arziki (GDP) ya kai kimanin dalai biliyan 906.
Kasar mamba ce a Kungiyar Kasashe Masu Karfin Tattalin Arziki ta G20 da Kungiyar OECD kuma tana bayar da gudunmowa wajen ayyuka ci gaba a duniya.
Tsakanin shekarun 2006 zuwa 2017, karkashin shugabancin Recep Tayyip Erdogan, kasar ta yi wasu sauye-sauye kuma ta samu ci gaba sosai, wanda ya sa aka ga samun arziki tsakanin mazauna kasar da kuma rage talauci da kashi 9.8 cikin 100. An samu raguwar adadin mutane da ke rayuwa a kasa da dala 6.85 a rana.
Turkiyya ita ce kasa ta biyar da ta fi kasancewa biyar ayyukan diflomasiyya a duniya, inda take da manya da kananan ofisoshin diflomasiyya 260 a kasar.
Tsarin shugaban kasa mai cikakken iko da kasar ta koma a kai a shekarar 2017 ya kawo sauyi tsarin siyasar kasar kuma hakan ya sa an kafa wata hadakar jam'iyyu biyu.
Daya daga cikin hadakar ana kiransa da People's Alliance wadda jam'iyyar AK ke jagoranta kuma sauran jam'iyyun da ke cikin wannan hadakar sun hada da jam'iyyar Nationalist Movement (MHP) da jam'iyyar Grand Union (BBP) da kuma jam'iyyar New Welfare (Yeniden Refah).
Sunan dayan hadakar Nation Alliance kuma ta kunshi jam'iyyun adawa ne. Jam'iyyar People's Party (CHP) ce take jagoranta. Hadakar ta kunshi jam'iyyar IYI Party da kuma jam'iyyun Saadet da Demokrat wadanda suke da magoya baya marasa yawa.
Yanzu wadannan hadaka biyu suna shirye-shiryen fafatawa a wannan muhimmin zabe na 2023. Recep Tayyip Erdogan yana neman wa'adi na biyu a matsayin dan takarar hadakar People's Alliance.
Babban abokin karawarsa shi ne Kemal Kilicdaroglu wanda jam'iyyarsa ta Republican People's Party (CHP) take bangaren hadakar National Alliance a babbar zaben Turkiyya na 2023.
Daga nan sai Sinan Ogan, malamin makaranta dan asalin kasar Azerbaijan, yana takararsa ne karkashin hadakar ATA Alliance a zaben watan Mayu, sai kuma jam'iyyar Memleket da ta gabatar da Muharrem Ince a matsayin dan takara na hadu a zaben Turkiyya na 2023.
Jam'iyyar AK Party ta kwashe shekaru 20 tana mulki kuma ta taimaka wa Turkiye kai wa babban matsayi a idon kasashen duniya saboda nasarorin da ta samu a fannoni da dama, wannan zaben yana da muhimmanci ga jam'iyyar saboda ta ci gaba da cimma muradun da ta sa a gaba.
Ga wasu daga cukin nasarorin da Turkiyya ta samu a shekaru 20 da suka wuce da kuma abubuwan da ta sanya a gaba kan wannan zabe.
Fasahohin zamani a fannin tsaro
Erdogan ya fara zama firaiministan kasar ne a shekarar 2003, inda cikin hanzari ya sauya fasalin tattalin arzikin kasar da fanni samar da ayyuka da fannin kere-kere kuma ya mayar da hankali sosai ga fannin tsaro da wasu muhimman fannuka da suka taimaka wa Turkiyya samun ci gaban kasa.
Tun daga nan ne Turkiyya ta samar da wasu tsare-tsaren da kuma rage dogaro da shigo da abubuwa daga kasashen ketare, inda aka mayar da hankali wajen samar da abubuwa a gida, musamman a fannin tsaro da kere-kere injina.
A shekaru 20, Turkiyya ta rage yawan dogaro da kasashen ketare a fannin tsaronta daga kaso 80 zuwa kaso 20 cikin 100.
Yayin da ake ci gaba da samun karin masu ruwa da tsaki da ke shiga fannin, fannin yana kara bunkasa, inda ake da kamfanonin tsaro fiye 1,500 idan aka kwatanta da guda 62 da ake da su a shekarar 2002 - kuma akwai ayyukan wasu 750 da ke tafe.
Bugu da kari, Turkiye ta ware dala biliyan 5.5 a matsayin kasafin kudin tsaro a shekarar 2002, yanzu ya kai dala biliyan 75 ciki har da wasu ayyuka da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi magana a kansu a baya-bayan nan.
A shekarar 2022, Turkiyya ta fitar da makamai da kayayyakin tsaro da kudinsu ya wuce dala biliyan uku kuma kudin zai kusan dala biliyan hudu zuwa karshen wannan shekara wanda ya sa za a iya kwatanta adadin kayan da kasar take fitarwa da na wasu kasashen nahiyar Turai - inda ya fi kasafin kudin da wasu kasashen Turai ke warewa a fannin tsaro.
A watan Oktoba, Sakataren Tsaron Birtaniya Ben Wallace ya bayyana jiragen yaki marasa matuka kiran Türkiye da cewa sun kawo sauyi a salon yaki na zamani.
Daya daga cikin manyan kamfanonin tsaro mai zaman kansa Baykar ya fara kera wani babban jirgi yaki mara matuki Bayraktar Kizilelma ko kuma Red Apple, inda kasashen duniya suka yaba da su.
Bayan ya kammala gwaji a watan Disamban bara, Kizilelma wata manuniya ce ta yadda kasar take samun ci gaba a fannin kere-kere jiragen yaki marasa matuka.
An yi hasashen babban jirgin yakin mara matuki zai ayyukan soja da dama kamar dabarun kai hare-hare da kai taimako ta sama da harba makami mai linzami da dakile hare-haren makiya ta sama da sauransu.
An yi hasashen babban jirgin yakin mara matuki zai ayyukan soja da dama kamar dabarun kai hare-hare da kai taimako ta sama da harba makami mai linzami da dakile hare-haren makiya ta sama da sauransu.
Tankar tana dauke da babbar bindiga Rheinmetall mai tsawon 120mm da wata bindiga kırar machine gun da kuma wata matsakaiciyar bindigar machine gun mai tsawon 7.62mm.
An tsarata ne saboda samar da karin kariya ga tankoki da sauran motoci masu silke daga barazana iri-iri.
Kari a kan wadannan nasarorin a fannin tsaro shi ne babban jirgin ruwan tsaro na TCG-Anadolu, wanda shi ne jirgin ruwa na farko a duniya da yake dauke da jiragen yaki marasa mayuka, wannan ne babban makamin yaki da Turkiyya ta taba kerawa.
Jirgin ruwan TCG-Anadolu ya fita daban ta fuskoki da dama kuma karin karfi ne ga rundunar sojin Turkiyya, kuma zai iya aiki tare da wasu jiragen yaki marasa matuka kamarsu Bayraktar TB-3 da Akinci da kuma Kizilelma har ma jirgin yaki na Hurjet.
Mafarkin Turkiyya na shekara 60
Motar Togg ita ce mota mai amfani da lantarki ta farko da kasar ta kera kuma wata manuniya ce kan yadda kasar ta samu ci gaba a fannin fasaha.
TOGG yana nufin Türkiye's Automobile Joint Venture Group a harshen Ingilishi ta fara yin gwajin kera mota mai amfani da lantarki ne a watan Disambar 2019. Kamfanin yana shirin kera motoci miliyan daya samfuri biyar daga nan da shekarar 2030.
TOGG ita ce mota kirar Turkiyya ta farko da ta samu kyautar iF Design Award a shekarar 2021, wannan wata babbar kyautar zayyane-zayyane ta duniya, TOGG ta samu kyautar ne da motarsu samfurin C-SUV.
Manyan kamfanoni na duniya sun bayyana bukatarsu ta zuba jari a fannin motoci masu aiki da lantarki, in ji Shugaba Recep Tayyip Erdogan yayin taron kaddamar da motar TOGG, ya ci gaba da cewa da taimakon Ma'aikatar Masana'antu da kuma Ma'aikatar Fasaha, Türkiye ta fara wani shiri na samar da tashohin cajin mota kimanin 1,500 a larduna 81 da ke kasar.
Gano iskar gas a Tekun Bahar Aswad
Turkiyya ta fara hako iskar gas da ta samu daga Tekun Bahar Aswad wanda hakan zai taimaka wa kasar dogaro da kanta a fannin makamashi.
Gabanin zabukan ranar 14 ga watan Mayu yayin kaddamar da fara aikin a garin Zonguldak Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce kowane gida zai samu iskar gas kyauta har na tsawon wata daya don murnar fara hako isakar gas din, kudin da kowane gida yake kashe kan iskar a kowane wata ya kai lira 625 wato kimanin dala 32.2.
A shekaru 20 da suka wuce Türkiye ta samu ci gaba sosai a fannin makamashi.
Kamfanin mai da iskar gas na kasar Turkish Petroleum (TPAO), ya sanar da kammala shinfida bututan iskar gas daga cikin tekun Bahar Aswad zuwa gaba tekun.
Turkiyya za ta biya bukatar da take da ita ta iskar gas da kaso 30 cikin 100 a kowace shekara daga tekun Bahar Aswad idan aka fara aikin sosai kuma hakan zai rage dogaro da kasar take yi kan wasu kasashe dangane da iskar gas.
Za a ba kowane gida kyautar 25 kubik mita na gas a kowane wata a tsawon shekara daya a wani kokari na kare 'yan kasa daga jin radadin tsadar farashin makamashi.
Samar da sauki ga miliyoyi
Wani muhimmin tsari da gwamnatin Erdogan ta yi a shekara 20 shi ne soke yawan shekarun ritaya.
Sabon tsarin ya shafi wadanda suka fara aiki kafin watan Satumbar shekarar 1999, lokacin da aka sauya dokar da take daidaita tanade-tanaden ritaya da kuma wadanda suka kai shekara 20-25 a bakin aiki.
Kamar yadda sabuwar dokar ta tanada an soke shekarun ritaya wanda a baya ake bukatar sai mace ta kai 58 yayin da namiji sai ya kai 60 - wannan ya bai wa fiye da ma'aikata miliyan biyu dama yin ritaya nan take.
Manufofin abokan hamayya
Yayin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan da kuma jam'iyyarsa ta Justice and Development Party suke bayyana nasarorin da suka samu a shekaru 20 da suka wuce, jam'iyyun suna daukar alkawuran da za su yi - ciki har da samarwa 'yan kasar damar yin tafiya ba tare da visa ba zuwa kasashen Turai - don samu goyon baya da yarda ga jama'ar Turkiyya.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sanar da manufofin jam'iyyarsa ta Justice and Development Party gabanin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a 2023.
Manufofin guda 23 sun mayar da hankali ne kan murmurewa daga girgizar kasar watan Fabrairu da sake gina birane na larduna 11 da samar da ayyuka miliyan 6 a kokarin rage adadin rashin aikin yi da kaso 7 cikin 100.
Recep Tayyip Erdogan ya kuma yi alkawarin cewa kasar za ta kara samun masu zuba jari da bunkasa yawon bude ido inda za a samu 'yan yawon bude ido miliyan 90 da samun kudin shiga dala biliyan 100 daga yawon bude ido. Masu zuba jarin sun hada da na fannin tattalin arziki da muhalli.
Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin kara karfin kasar a fannin makamshi da aikin gona da ilimi da sufuri da manufofin kasashen waje inda za a mayar da hankali kan samar da zaman lafiya.
Yadda ake zabe a Turkiyya
A ranar 14 ga watan Mayu, 'yan Turkiyya za su je rumfunar zabe don zabar shugaban kasa 'yan majalisa. Mutane da yawa suna ganin wannan zaben yana da muhimmanci sosai a tarihin kasar na baya-bayan nan.
Ana zabar shugaban Turkiyya ne ta zabe zagaye biyu, inda dole dan takara ya samu kuri'u mafi rinjaye ko kuma fiye da kaso 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada a duk fadin kasar.
Zaben Shugaban Kasa
Mutum hudu sun samu sa hannun mutum 100,000 da suke bukata kafin su iya tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2023.
Idan babu dan takarar da ya samu kuri'u mafiya rinjaye a zagayen farko, to za a je zagaye na biyu a ranar 28 ga watan Mayun 2023. Babban Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe (YSK) ce za ta sanar da sakamakon bayan kidaya kuri'un.
Wurin da ya fi ko ina yawan 'yan Turkiyya shi ne Yammacin Turai, inda ma'aikatan Turkiyya suke zaune tun bayan yakin Duniya na Biyu a shekarar 1960. Su ne al'ummar 'yan ci- rani Musulmi mafi yawa a Yammacin Turai.
'Yan Turkiyya mazauna kasashen waje za su fara zabe ne tsakanin ranakun 27 ga watan Afrilu zuwa 9 ga watan Mayu, yayin da za a yi zaben a Turkiyya ne ranar 14 ga watan Mayu.