A watan Yulin da ya gabata ne Turkiyya da Masar suka ƙulla hulɗar diflomasiyya tare da naɗa jakadu. / Hoto: AA

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce yunƙurin korar al'ummar Gaza na Falasdinu daga yankunansu da Isra'ila ke yi ba shi da amfani kuma ba zai yi tasiri ba.

Erdogan ya ce "ba za a amince da tilastawa al'ummar Gaza ba," a yayin wani taron manema labarai da ya yi da takwaransa na Masar Abdel Fattah el Sisi a birnin Alkahira a ranar Laraba.

"Abin da muka fi baiwa fifiko shi ne mu cimma tsagaita wuta da wuri-wuri don isar da kayan agaji zuwa Gaza ba tare da wani cikas ba," in ji shi.

Har ila yau, ya ƙara da cewa, Turkiyya za ta ci gaba da ba da haɗin kai da kuma tsayawa tsayin daka da "ƴan'uwanta na Masar" don kawo karshen zubar da jini a Gaza.

A watan Yulin da ya gabata ne Turkiyya da Masar suka ƙulla hulɗar diflomasiyya tare da naɗa jakadu.

Dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta kasance a ƙaramin mataki tun shekarar 2013.

AA