Sashen kula da sararin samaniyar Turkiyya ya samu wani gagarumin ci gaba mai cike da tarihi, inda kamfanonin ƙasar biyu da ke ƙera jiragen sama wato TAI da Baykar suka shiga jerin manyan kamfanonin jiragen sama 50 na duniya, bisa ga kiɗiddigar kuɗaɗen shigarsu ta shekarar 2023 wadda hukumar leƙen asiri ta Counterpoint Market na FlightGlobal ta fitar.
Kamfanin TAI na matsayi na 38, inda ya ba da rahoton samun dala biliyan 2.67 na kuɗaɗen shigarsa, yayin da Baykar ke a matsayi na 49 da dala biliyan 1.8.
Matsayin TAI na 38 na nuna irin ci gaba da ya ke samu, inda ya samar jiragen masu saukar angulu ƙirar ANKA lll, da HURJET da kuma jirgin yaƙi na KAAN.
TAI ya fice wajen samar da manyan fasahohi na zamanin tare da ci gaba a fannin bincike, da kuma mayar da hankali wajen fitarwa da kuma samar da tsarin samfuran fasahohi ga manyan kamfanonin jiragen sama.
Haɗin gwiwar kamfanin tare da fitattun kamfanoni a harkar kusawancin jiragen sama masu zaman kansu da na sojoji a duniya ya karfafa masa yin fice.
Baya ga manyan samfuran kayayyakin tsaro da yake samarwa, haɗin gwiwar TAI da sauran kamfanoni masu zaman kansu a fannin jiragen sama ya ƙarfafa rawar da ya ke takawa a matsayin mai mahimmanci wajen samar da manyan fasahohi.
Matsayin Baykar na farko a jerin
Baykar, wani babban kamfani ne a fannin kasuwanin kera jirage marasa matuƙi (UAV), yana matsayi na 49 a jerin inda kudaden shigar da ya samu a 2023 ya kai dala biliyan 1.8.
Ya yi fice a samfurin jirginsa na Bayraktar TB2, kazalika kamfanin ya yi suna wajen fitar da jiragen yaki marasa matuki a duniya, tare da fasaharsa da ake buƙata a duk faɗin duniya.
Baykar ya sanya hannu kan yarjejeniyar fitar da kayayyakinsu zuwa kasashe 35 kan samar da jiragensa ƙirar Bayraktar TB2 da Bayraktar AKINCI UAVsƙ
Fiye da kashi 90 cikin 100 na kudaɗen da kamfanin ya samu ya fito ne daga fitar da kayayyakinsa zuwa ƙasashen duniya, Baykar ba kawai ya tsaya wajen fayyace fannin tsaron Tukiyya ba ne, yana riƙe da matsayinsa na babban kamfanin da ke fitar da kayyaykin tsaro na ƙasar mai fitar a tsawon shekaru uku a jere.
Dukka kamfanonin biyu, TAI da Baykar suna ci gaba da saka hannun jari a sabbin fasahohi.
TAI yana ci gaba da ƙera jiragen yakinsa na KAAN, yayin da Baykar ke mai da hankali wajen samar da jiragen yaki marasa matuka ƙirar Bayraktar TB3, da jirgin ruwa mai saukar ungulu ƙirar UAV, da kuma Bayraktar Kizilelma da ake sa rai samarwa wato jirgin yaki na sama na farko na Turkiyya.
Ci gaba a kasuwanin duniya
Matsayin dai, ya sanya TAI da Baykar a cikin jerin manyan kamfanoni kamar Boeing da Airbus, waɗanda bi da bi suke kan gaba a jerin kudaɗen shigar kamfanonin ƙera jiragen samana duniya da dala biliyan 77.8 da kuma dala biliyan 70.8.
Manyan kamfanonin da ke kan gaba a jerin sun fito ne daga Amurka da ƙasashen Turai, yanayin da ke nuni da irin rinjayen da kamfanonin Amurka da na Turai a fannin sararin samaniya, musamman waɗanda suka mayar da hankali wajen samar da fasahohin tsaro da na farar hula.
A bana dai, manyan kamfanoni irin su RTX, da Lockheed Martin, da Northrop Grumman suna ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fannin masana'antar tsaron Amurka a duniya.
Ko da yake, bayyanar kamfanoni irin su Baykar da TAI na nuna sauyin da ake samu a wannan ɓangare, inda kamfanonin waɗanda ba na ƙasashen Yammacin Turai ba suke shiga jerin da kamfanonin ƙasashen Yamma suka mamaye.