Shugaban ƙasar Turkiyya ya soki yadda ƙasashen Musulmai ba sa mayar da isasshen martani wajen magance kisan ƙare dangin da Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza, yayin da ya soki ƙasashen Yamma kan bai wa Isra'ila cikakken goyon baya a yaƙin.
"Wasu Ƙasashen Yammacin duniya ƙalilan ne suka bai wa Isra'ila kowane irin tallafi, yayin da gazawar Ƙasashen Musulmi wajen mayar da martani mai inganci ya sa lamarin ya kai ga wannan matsayi," in ji Racep Tayyip Erdogan a ranar Litinin a wajen Babban Taron Ƙolin Hadin Gwiwa na Ƙungiyar Hadin Kan Musulunci (OIC) da Ƙungiyar ƙasashen Larabawa a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya.
Erdogan ya ce zuwa yanzu Turkiyya ta iaka sama da ton 84,000 na kayan agaji zuwa Gaza, kuma a shirye take ta ƙara aika wasu idan aka ɗage takunkuman da aka sanya.
Isra'ila ba za ta iya ko da bari a kai kayan agaji Gaza ba, kuma ta sa an shafe watanni ana jiran a shigar da kayayyakin waɗanda ke Masar, Erdogan ya ƙara da cewa.
A shirye muke mu aiwatar da dukkan wasu matakai da za su nuna irin girman mamayar da gwamnatin NEtanyahu ke ci gaba da yi a yankin Falasɗinawa, in ji Shugaban Ƙasar Turkiyyan.
"Ya kamata mu ƙarfafa wa ƙasashe da dama don su shiga cikin shari'ar da Afirka ta Kudu ta shigar da Isra'ila a Kotun Duniya," ya jaddada.
Rikicin yanki ya ta'azzara saboda zalincin da Isra'ila ke yi a Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 43,600, mafi yawansu mata da yara, sakamakon harin da ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas ta kai a bara.
A yayin da rikicin ke yaɗuwa zuwa Lebanin inda Isra'ila ke ƙaddamar da hare-hare a faɗin ƙasar, kusan mutum 3,200 aka kashe sannan fiye da 13,800 suka jikkata a hare-haren na Isra'ila tun daga bara, a cewar hukumomin lafiya na Lebanon.
Duk da gargaɗin ƙasashen duniya cewa yankin Gabas ta Tsakiya na dab da faɗa wa cikin yaƙi, Tel Aviv ta faɗaɗa rikicin ta hanyar ƙaddamar da hare-hare ranar 1 ga wata Oktoba da kuma kutsawa kudancin Lebanon.