Yau Alhamis ‘yan Turkiyya da ke zaune a kasashen waje sun soma kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki wanda za a fara a Turkiyya ranar 14 ga watan Mayu.
Turkawa mazauna kasashen waje sun fara kada kuri’a a rumfunan zabe 156 da aka bude a kasashe 73.
An bude rumfunan zabe a shingen jami’an kwastam na kan iyakokin kasar, inda aka ajiye akwatunan zabe ga masu kada kuri'a ba tare da sun yi shiri na musamman ba.
An fara jefa kuri’a da karfe 5 na asubar Alhamis a agogon GMT, kuma an shirya rufe rumfunan zaben zuwa karfe 2 na rana agogon GMT duk rana.
Zaben-wurin zai zo karshe ne ranar 9 ga watan Mayu a rumfunan zabe, sai kuma ranar 14 ga watan na Mayu a kawo karshen kada kuri’a a shingen jami’an shige da fice.
Su waye suka fara zaben-wuri?
Akwai masu rajistar yin zabe sama da miliyan 3.4 a wajen Turkiyya. Adadin masu zaben wadanda za su kada kuri’a a karon farko ya kai 277,646.
An ajiye akwatuna 4,671 a bakin shingen jami’an kwastam.
A karon farko a wannan shekara, Hukumar Koli ta Zaben Turkiyya za ta bude rumfunan zabe a kasashen Belarus, Brazil, Pakistan, Portugal, Slovakia, da Tanzania.
Jamus ce ta fi yawan ‘yan Turkiyya masu yin zabe
A kasashen da aka bude rumfunan zabe, Jamus ce take da adadi mafi yawa na ‘yan Turkiyya masu kada kuri'a a zaben shugaban kasa, yayin da Brazil take da adadi mafi karanci.
Sama da masu zabe sama da miliyan 1.5 za su jefa kuri’a a rumfunan zabe 26 a Jamus. Sai kuma Faransa mai masu zabe 397,086 a rumfuna tara, sannan kuma Netherlands mai masu zabe 286,753.
A Amurka kuwa, sama da mutane 134,000 ne za su kada kuri'a a rumfuna tara.
Haka nan bayanin hukumar zaben sun nuna cewa kasar da take da adadin ‘yan Turkiyya mafi karanci ita ce Brazil mai masu zabe 581, sai kuma Nijeriya da masu zabe 584.
Bayan kammala zaben, idan babu dan takarar da ya ci sama da kashi 50 na kuri’u, za a tafi zagaye na biyu, wanda za a yi ranar 28 da watan Mayu, sai kuma ranar 20-24 ga Mayu a rumfunan kasashen waje.