Rikicin Gaza ya fara ne a ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta kaddamar da Operation Al Aqsa. / Hoto:  AA  

Hukumar kwallon kafa ta Turkiyya TFF ta ce za a yi shiru na wasu 'yan lokuta kafin a fara buga wasannin gasar bana don nuna alhini kan mawuyacin halin da yankin Falasdinu ke ciki

Kazalika hukumar ta ce 'yan wasan za su bayyana a fili sanye da bakaken riguna.

Yankin Gaza na fuskantar hare-haren bama-bamai da kuma mamayar Isra'ira tun shekarar 2007.

Lamura sun dakule a yankin tun daga ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta kaddamar da Operation Al Aqsa - harin ba-zata da ta harba rokoki tare da kutsa kai cikin yankin Isra'ila ta hanyar kasa da teku da kuma ta sama.

Hamas ta ce ta dauki mataki ne a matsayin ramuwar gayya ga harin da aka kai Masallacin Kudus da kuma karuwar cin zarafi da matsugunawar Isra'ila a Falasdinawa.

Daga nan ne sojojin Isra'ila suka kaddamar da Operation Sword of Iron a kan mayakan Hamas da ke Gaza.

Akalla Falasdinawa 3,785 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai Gaza, yayin da a bangare guda adadin mutanen Isra'ila da suka mutu ya kai 1,400.

TRT World