Erdogan ya jaddada cewa shigar da Turkiyya ta yi a Cyprus a shekarar 1974 aiki ne na zaman lafiya da nufin kawo karshen kisan kiyashi da kuma mayar da zaman lafiya, daidai da dokokin kasa da kasa.   / Hoto: Others

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa babu batun wata sabuwar tattaunawa a Cyprus a halin yanzu har sai ɓangarorin da ke tsibirin sun zauna sun tattauna a matsayinsu "na ɗaya."

"A gaskiya ba mu ga wata alamar soma wata sabuwar tattaunawa ba a Cyprus ba tare da ɓangarorin biyu sun zauna a teburi ba a matsayin ɗaya," kamar yadda Erdogan ya shaida wa manema labarai a jirginsa na komawa gida bayan ya kai ziyara Arewacin Cyprus ta Jamhuriyar Turkiyya.

A yayin da yake magana dangane da kalaman Ministan Tsaron Girka Nikos Dendias wanda ya kira Turkawa "masu mamaya," Erdogan ya bayyana cewa kalaman "ba za su zama rashin kunya ba," inda yake kira ga Firaministan Girka Kyriakos Mitsotakis ya sa Dendias ya "shiga hankalinsa."

Erdogan ya sake jaddada cewa shigar da Turkiyya ta yi a Cyprus a shekarar 1974 aiki ne na zaman lafiya da nufin kawo karshen kisan kiyashi da kuma mayar da zaman lafiya, daidai da dokokin kasa da kasa.

Erdogan ya bayyana cewa, shi da firaministan kasar Girka Kyriakos Mitsotakis sun amince a taron kungiyar tsaro ta NATO na karshe kan kauce wa kalaman ɓatanci yayin ziyarar da suke a kasar Cyprus.

"Rundunar sojan Turkiyya na da tarihi mai kyau na rashin zaluntar ko da makiyanta ne kuma ba ta tauye hakkin wadanda aka zalunta. Za ta ci gaba da aiki da irin wannan fahimta a yau da kuma nan gaba. Su sani cewa a kasashen da sojojinmu suka saka kafarsu, akwai zaman lafiya ba wai mamaya ba."

Mayar da hankali kan ababen more rayuwa ba sansanonin soji ba

Da yake tattaunawa game da ci gaban soja da dabaru, Erdogan ya lura cewa Arewacin Cyprus na gina sabuwar fadar shugaban ƙasa da kuma majalisar dokoki, yana mai nuna yadda Turkiyya ke mayar da hankali kan ababen more rayuwa na siyasa maimakon sansanonin soji.

Ya soki shirin da ake yi na kafa sansanin sojojin ruwa da ƙasar Cyprus ta Girka da kawayenta ke yi, yana mai gargadin cewa hakan na iya kara dagula al'amura, inda ya ce: "Idan ta kama, za mu iya gina sansanin sojan ruwa a arewaci,"

Ya kamata a kauce wa matakan da ba za su taba taimakawa wajen samar da zaman lafiya a tsibirin ba, da kara tashe-tashen hankula da haifar da keta dokokin kasa da kasa. Kasancewa abokin tarayya a kisan kiyashin da ake yi a Isra'ila ba zai amfanar da Girkawa ko Girka da komai ba," kamar yadda ya yi gargaɗi.

Erdogan ya kuma bayyana shirin samar da wani sabon wuri na samar da iskar gas na Turkiyya, inda ya kwatanta shi da wani muhimmin wuri, ya kuma bayyana yadda Turkiyya ke ci gaba da samun 'yancin kan makamashi.

TRT World