Turkiyya ta yi "kakkasar kusa" ga Sweden bisa kyale kungiyar ta'addanci ta PKK ta yi amfani da sabon salo na tunzarawa kan shugaban kasa Recep Tayyip Erdogan.
"Mun yi Allah wadai da kakkausar murya game da barin kungiyar da ke da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta PKK ta watsa farfaganda ta hanyar amfani da alamun ta'addanci sannan ta muzanta shugaban kasarmu," a cewar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ranar Asabar.
Kazalika ma'aikatar ta tuna wa gwamnatin Sweden alkawarin da ta yi na hana ayyukan kungiyar 'yan ta'adda ta PKK da kungiyoyi masu alaka da ita.
Da fari dai, wasu masu goyon bayan kungiyar 'yan ta'adda ta YPG/PKK sun harzuka Turkiyya ta hanyar yawo da mutum-mutumin Shugaba Erdogan wanda suka sanya wa alamomin masu auren jinsi daya a wani taro da suka yi a Stockholm, babban birnin Sweden.
Mutanen da ke rike da kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce da tambarin YPG/PKK sun yi zanga-zangar da ke adawa da neman da Sweden take yi na shiga kungiyar tsaro ta NATO.