Ankara ta bukaci kasashen Turai su kawo karshen farfaganda da kudade da kuma daukar ma'aikata na kungiyar ta'addanci ta PKK, sakamakon sabon kutsen da take yi yi. / Hoto: AA

Turkiyya ta yi Allah wadai da yunkurin wasu mutane da ke da alaka da kungiyar ta'addanci ta PKK wajen tilasta wa kansu shiga ginin kotun kare hakkin bil adama ta Turai da ke Strasbourg a arewacin kasar Faransa don yada farfagandar ta'addanci.

A ranar Alhamis Ankara ta fito ta yi tir da lamarin tana mai cewa "ba za a amince da hakan ba".

Kungiyoyin 'yan ta'addan, wadanda ke da alaka ta kusanci da PKK, na kara kaimi wajen kai hare-hare, inda suke kutsa kai da karfin tsiya cikin ofisoshin kungiyoyin kasa da kasa a nahiyar Turai, a wani yunkuri na yada farfagandar ta'addanci, a cewar sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta fitar.

"Bai wa PKK 'yancin gudanar da ayyukanta (ba takura), musamman a kasashen Turai, a karkashin inuwar 'yancin fadin albarkacin baki da zanga-zanga yana karfafa gwiwa ga kungiyar wajen aiwatar da ayyukan da suka sabawa doka, in ji ma'aikatar.

Ankara ta jaddada kiranta ga kasashen turai don kawo karshen duk wasu ayyukan PKK na yada farfaganda da samun kudadensu da kuma daukar ma'aikatan kungiyar daga yanzu.

Sanarwar ta kuma tunatar da gargadin da Ankara ya yi a baya game da zanga-zanga da ayyukan da 'yan ta'addar PKK suka yi a kusa da ginin majalisar Turai, tare da jaddada cewa irin wadannan ayyuka na nuna irin barazanar da 'yan ta'addar ke yi ga zaman lafiya da tsaro a duk kasar da suka samu mafaka.

A sama da shekaru 35 da take gangamin aiwatar da ta'addanci a kan Turkiyya, PKK - wadda Turkiyya da Amurk da Tarayyar Turai suka sanya a matsayin kungiyar ta'addanci - ta dauki alhakin mutuwar sama da mutane 40,000, ciki har da mata da yara da kuma jarirai. YPG ita ce reshenta a Siriya.

TRT World