Kalaman na daraktan sadarwa sun zo bayan da aka kashe wani dan jarida mai zaman na Anadolu Montaser Al-Sawaf a hare-haren da Isra'ila ta kai./ Photo: AA Archive

Turkiyya ta yi Allah-wadai da harin da Isra'ila ta kai da gangan tare da kashe wani dan jarida mai daukar bidiyo da ke yi wa kamfanin dillancin labaran Anadolu na Turkiyya aiki a matsayin ma'aikaci mai zaman kansa, da ke aiki daga Gaza.

"Dubban mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ne suka rasa rayukansu a kisan gillar da Isra'ila ta shafe tsawon watanni biyu tana yi.

Kasancewar akwai 'yan jarida 72 da ke aikinsu a cikin wadannan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da suka rasa rayukansu, wata alama ce da ke nuni da cewa da gangan Isra'ila ke kai hari kan 'yancin fadin albarkacin baki," kamar yadda Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya wallafa a shafin X ranar Juma'a.

Kalaman nasa sun zo nei bayan da aka kashe wani ɗan jarida mai zaman kansa na Anadolu, Montaser Al-Sawaf a harin da Isra'ila ta kai.

“Dole ne kasashen duniya da kafafen yada labarai su dauki kwararan matakai ba tare da ɓata lokaci ba domin daƙile wadannan kashe-kashe da gaggawa.

"Mun sake yin Allah wadai da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi da kuma cin zarafin 'yan jarida da gangan wanda ke yin sanadin mutuwarsu," in ji Altun.

Ya kuma jajantawa iyalan Al-Sawaf, da abokan aikinsa, da kuma kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

An kashe mai daukar hoton Anadolu

An kashe Montaser Al-Sawaf, wani dan jarida mai zaman kansa da ke daukar bidiyo yake kuma aika rahoto ga Anadolu, a Gaza a ranar Juma'a, a hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama, bayan komawa fagen daga da bangarorin biyu da ke yaki suka yi, sakamakon karewar yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda.

Hassan Ismameh, ɗan'uwan dan jaridar ya shaida wa Anadolu cewa "Sawaf, da ɗan'uwansa Mervan, da wasu 'yan'uwa sun yi shahada a lokacin da Isra'ila ta kai hare-hare a yankin Ed-Durc da ke kudancin Gaza."

Bayan ya samu munanan raunuka sakamakon tashin bam din, sai da Al-Sawaf ya jira motar daukar marasa lafiya na kusan rabin sa'a, in ji shi.

Daga karshe dai an dauke Al-Sawaf zuwa Asibitin Baptist na Al-Ahli da mota mai zaman kansa bayan babu wata tawagar likitoci da ta zo, in ji Ismameh.

An yi jana'izar Al-Sawaf tare da wasu 'yan'uwansa da aka kashe a harin na Isra'ila, a maƙabartar al-Batsh da ke birnin.

'Bama-bamai sun fada kan darajar Ƙasashen Yamma'

Serdar Karagoz, Shugaban Kamfanin Anadolu, ya mika sakon ta'aziyyarsa a cikin wata sanarwa, yana kuma yin Allah wadai da cewa, ya zuwa yanzu, an kashe 'yan jarida 71 a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza.

Karagoz ya ce "A Anadolu, muna fafutuka ne don tabbatar da tsaron abokan aikinmu da ke gudanar da ayyukansu a cikin mawuyacin hali a Gaza cike da ƙwazo."

"A madadin dukkan abokan aikinmu da suka rasa rayukansu a hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai a Gaza, ciki har da jami'in hukumarmu mai zaman kansa Montaser Al-Sawaf, za mu ci gaba da fafutukar da muke yi ta ganin an hukunta wadanda ke da alhakin wadannan hare-haren a karkashin dokokin kasa da kasa," ya kara da cewa.

Karagoz ya miƙa ta'aziyyarsa ga daukacin 'yan jaridar da suka rasa rayukansu a Gaza, yana mai jajantawa iyalansu.

“A yau, bama-baman da gwamnatin Isra’ila ta harba kan Falasdinu ba wai kan yara Falasdinawa ba ne kawai ko asibitoci ko makarantu ko masallatai, da coci-coci ba, har ma da dabi’un Ƙasashen Yamma, da dokokin ƙasa da ƙasa, da ‘yancin ɗan'adam, da duk wani abu da ke nuni da alheri,” in ji shi.

"Yana wargaza wadannan dabi'u, kuma kasashen duniya, wadanda ya kamata su kiyaye wadannan dabi'u, na daya daga cikin wadanda suka fi yin rashin nasara a Gaza."

Da take bijirewa kiran da kasashen duniya suka yi na tsagaita wuta, rundunar sojin Isra'ila ta sanar a safiyar yau Juma'a cewa ta sake kai hare-hare a Zirin Gaza, yayin da aka kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wutan da aka yi ta tsawon mako guda.

An fara tsagaita wutar ne da safiyar ranar 24 ga watan Nuwamba a matsayin wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Isra'ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, na dakatar da fadan na wani dan lokaci don ba da damar sakin wadanda aka yi garkuwa da su da fursunoni daga bangarorin biyu, da kuma kai kayan agaji.

Fiye da Falasdinawa 15,000 galibi yara da mata ne aka kashe a hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga watan Oktoba. Kuma an kashe ‘yan Isra’ila kusan 1,200 a cewar alkalumman hukuma.

TRT World