Matsayar da Senegal ta ɗauka game da batun Falasɗinu, wanda ke da burin samar da ƙasashe biyu yana da matuƙar muhimmanci, cewar Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan.
“Muna bibiyar jajirtacciyar matsayar da 'yan uwanmu a Afirka suka ɗauka, na fahimtar ma'anar zalunci, yaƙi, da kuma kisan kiyashi, dangane da tsarin Isra'ila na kisan ƙare-dangi,” Shugaba Erdogan ya faɗa ranar Alhamis a taron manema labarai da ya yi tare da takwaransa na Senegal, Bassirou Diomaye Faye.
Matsayar Senegal game da batun Falasɗinu, na samar da ƙasashe biyu yana da matuƙar muhimmanci, cewar Erdogan.
“'Yan mulkin mallaka a Afirka sun gano cewa makoma mai cike da zaman lafiya ba a gina ta da jinanen jama'a da kisan kiyashi,” in ji Erdogan, wanda ya ƙara da cewa: “Irin wannan gaskiyar za ta sake bayyana a Gaza da Lebanon.”
Game da hare-haren Isra'ila a Lebanon da Falasɗinu, shugaban na Turkiyya ya ce yankin "na tunkarar babbar gobara," inda ya yi gargaɗin cewa zamanin da ke tafe zai zama mafi fuskantar matsala.
Shugaba Erdogan ya kuma nemi duka ƙasashe da ke da “sanin yakamata” su saka matsin lamba kan gwamnatin Isra'ila.