Akalla mutum 10,000 ne suka jikkata a hare-haren baya-bayan nan da aka kai a Gaza, da dama sun cika makil a asibitoci shida da suka rage a yankin. / Photo: AA

A martanin Turkiyya kan mummunan harin da aka kai Asibitin Al Ahli Arab da ke Gaza, Ministan Harkar Lafiya na ƙasar, Fahrettin Koca ya bayyana cewa Ma'aikatar Lafiya ta Turkiyya ta ɗauki matakin gaggawa don samar da agajin ayyukan kiwon lafiya a Gaza.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a shafinsa na X kan cewa ana ci gaba da tattauna hanyoyin kai agaji zuwa yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya, tare da wasu ƙungiyoyin kiwon lafiya na ƙasa da ƙasa.

Aƙalla mutum 500 ne suka mutu a harin da wasu jiragen yaƙin Isra’ila suka kai kan Asibitin Al Ahli Arab da ke Gaza da yammacin ranar Talata.

Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna gawarwakin da aka baza a harabar shiga asibitin.

Ministan na Turkiyya ya ce ya jagoranci zantawar diflomasiyya ta wayar tarho da wasu ƙungiyoyin ƙasashen waje ciki har da manyan jami'an Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, yana mai cewa "ba za a amince da kai hari wuraren da ake kula da lafiyar al'umma ba a kowane irin yanayi ko dalili."

"Ba zai taɓa yiwuwa mu ci gaba da yin shiru kan wannan harin ba.'' Nauyin rashin taimakon marasa lafiya da waɗanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba yana wuyanmu, musamman la'akari da cewa wani ɓangare na duniya ya yi watsi da hakan," a cewar sanarwar ta Koca.

Koca ya ƙara da cewa, a shirye Turkiyya take ta aika jirgin ruwanta na asibiti zuwa yankin ko kuma ta kafa asibitocin wucin gadi a Gaza ko ku a kusa da kofar iyakar Rafah.

Hadin kan Turkiyya da WHO

A yayin zantawarsa da Dr Hans Kluge daraktan hukumar lafiya ta WHO a nahiyar Turai, Koca ya jaddada muhimmancin gaggauta tallafawa yankin Gaza da muhimman kayayyakin kiwon lafiya tare da bayyana aniyar hadin kan Turkiyya da hukumar WHO.

Kluge ya mayar da martani ga Koca ta shafin X inda ya godewa Ma'aikatar Lafiya ta Turkiyya bisa hadin gwiwar da suka yi, yana mai cewa "WHO da sauran abokan aikin jinƙai suna ƙoƙari wajen tabbatar da cewa magunguna da sauran kayayyaki kiwon lafiya sun isa ga marasa lafiyan da ke bukata," in ji shi.

"Shirin aikin hadin gwiwarmu kan wannan ƙuduri na ci gaba da tafiya yadda ya kamata," in ji shi.

Ministan na Turkiyya ya kuma jaddada cewa, duk da matsalolin diflomasiyya da ƙasar ke fuskanta, ''Turkiyya za ta ci gaba da kai taimakonta ga yara da jarirai da tsofaffi da kuma sauran mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.''

" Muna cikin wani zamani da mutane ke da zaɓin iya taimako ko ƙin taimakon rai."

Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu wacce hedikwatarta ke Gaza ta ce Asibitin Al Ahli Arab na ba da mafaka ga ɗaruruwan marasa lafiya da waɗanda suka jikkata da kuma sauran mutanen da "aka tilasta musu barin gidajensu" sakamakon hare-haren Isra'ila.

An mayar da hankali kan asibitocin ne la'akari da cewa su kadai suka tsira daga hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke kai wa yankin Gaza a kowace rana tun daga 7 ga watan Oktoba.

WHO ta ce an kai hare-hare kan gine-ginen kiwon lafiya 111 an kuma kashe ma'aikatan kiwon lafiya 12, sannan a cikin kwanaki 11 an kai hari kan motocin ɗaukar marasa lafiya 60.

Kimanin mutum 3,000 ne suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta kai, a cewar sanarwar hukumomi a Gaza.

Karancin kayayyakin kiwon lafiya da magunguna sun ƙara tsananta matsalar rashin ruwa da man fetur da za su taimaka wajen ci gaban ayyuka a cibiyoyin kiwon lafiya.

TRT World