Turkiyya ta kawar da 'yan ta'adda 45 a Syria da Iraki bayan kashe sojojin kasar shida a wani hari na ta'addanci. / Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jagoranci wani taron tsaro a ofishinsa na Dolmabahce da ke birnin Santambul.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da Ministan Harkokin Cikin Gida Ali Yerlikaya da Ministan Tsaro Yasar Guler da Shugaban Ma’aikata Metin Gurak da Shugaban Hukumar Leken Asiri Ibrahim Kalin da Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun da Shugaban Tsare-Tsare da Shawara kan Tsaro Akif Cagatay Kilic duk sun halarci taron, kamar yadda Ma’aikatar Sadarwa ta Turkiyya ta sanar a ranar Asabar a wata sanarwa.

Wannan na zuwa ne bayan an kashe sojojin Turkiyya shida a wani hari da ‘yan ta’addan PKK suka kai a arewacin Iraki a ranar Juma’a.

A yayin wannan taro na tsaro, shirye-shiryen dakile ta’addanci na kasar, musamman wurin mayar da martani kan harin ta’addanci na baya-bayan nan da aka kai arewacin Iraki, da kuma hanyoyin da za a bi wurin yaki da ta’addanci na daga cikin abubuwan da aka duba a yayin taron.

A yayin da aka kammala taron, an jaddada bayar da himma wurin ci gaba da yaki da ‘yan ta’addan PKK/YPG/KCK da kuma magoya bayansu duk a cikin tsarin dakilewa da kawar da duk wata barazana daga tushe.

Bayan kai wannan harin, Turkiyya ta kai samame wanda hakan ya sa ta kawar da ‘yan ta’adda 45, inda ta kawar da 36 a arewacin Iraki sai kuma tara a arewacin Syria, kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

Hukumomin sun jaddada cewa za a ci gaba da gudanar da wadannan ayyukan har sai an kawar da ta’addanci a Iraki da Syria, kamar yadda suka bayyana a wannan taron.

Kungiyoyin ta’addanci na PKK/YPG/KCK sun tafka babbar asara a ci gaba da yaki da ta’ddanci da Turkiyya ke gudanarwa a kan iyakokinta.

Sanarwar ta kara da cewa, yayin da kungiyar 'yan ta'addar ke fuskantar karin matsin lamba a kasashen Syria da Iraki, yunkurin farfado da kungiyar ya kara karfi.

“Babu shakka, ba za mu yarda a kafa kasar ‘yan ta’adda a kan iyakokinmu na kudanci ba, domin abin da muka sa a gaba shi ne mu lalata kogo, matsuguni da kuma gine-ginen ‘yan ta’adda,” kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

Turkiyya ta kaddamar da shirinta na Operation Claw-Lock a Afrilun 2022 domin yaki da ‘yan ta’addan PKK a maboyarsu da ke arewacin Metina da Zap da Avasin-Basyan kusa da iyakokin Turkiyya.

TRT World