A daidai lokacin da ake ci gaba da samar da mahajojin ƙirƙirarriyar basira, daraktan watsa labaran Turkiyya ya yi gargaɗi dangane da ƙalubalen da ake fuskanta wurin bambanta abubuwan da bil'adama ke samarwa da kuma wanda ƙirƙirarriyar basira ke samarwa. / Hoto: AA Archive

Daraktan Watsa Labarai na Trukiyya Fahrettin Altun ya yi gargaɗi dangane da matsalolin da ake samu a duniya ta ɓangaren adalci a watsa labarai inda ake danniya ga kafafen watsa labarai kuma kafafen watsa labarai na ƙasashen Yamma na yada farfaganda da kuma samar wa rashin adalcin gindin zama.

A yayin da yake magana a wani taro dangane da satar fasahar labarai da kuma amfani da ƙirƙirarriyar basira a kafafen watsa labarai, Altun ya jaddada cewa waɗannan kamfanonin "na ɗaukar labarai na ainahi da kuma bayanai daga faɗin duniya, inda suke rarraba su ta siffa daban-daban domin samun riba," da kuma samar da rashin adalci.

Altun ya yi kira kan a bayar da kariya ga labarai a ƙarƙashin dokokin kiyaye satar fasaha domin kiyaye labarai na asali. Haka kuma ya bayar da shawarar samar da sabuwar dokar kiyaye satar fasaha ta zamani domin magance matsalolin labaran ƙarya waɗanda suke kawo cikas ga dimokuraɗiyya.

Ilollin ƙirƙirarriyar basira

Altun ya jawo hankali dangane da yadda ake ƙara amfani da ƙirƙirarriyar basira a kafofin watsa labarai, inda ya jaddada hatsarin da ke tattare da keta sirri da da satar bayanai da yin labarai na ƙarya.

Ya yi gargaɗi kan cewa babban hatsarin da ke tattare amfani da ƙirƙirarriyar basira a ɓangaren watsa labarai shi ne mayar da hankali kan labarai masu jawo hankali a maimakon ainahin labarai masu inganci, inda maimakon a nemi ƙarin bayani a labarai masu muhimmanci sai a koma wurin masu jawo hankali.

TRT World