Tun daga farkon wannan shekara an hana mutum 65,225 wucewa ba bisa ƙa'ida ba. / Hoto: AA Archive

Ma'aikatar Tsaron kasar Turkiyya ta sanar da cewa tun daga farkon shekarar 2024 sojojin Turkiyya sun kashe 'yan ta'adda 1,427 a hare-haren da suke ci gaba da kaiwa.

Kakakin Ma'aikatar Birgediya Zeki Akturk ya yi ƙarin bayani a wani taron manema labarai a jiya Alhamis cewa, dakarun Turkiyya na ci gaba da yaƙar duk wata barazana da suka hada da kungiyoyin 'yan ta'adda na PKK/KCK/PYD-YPG da Daesh da kuma FETO.

"Dakarunmu na Turkiyya sun kashe 'yan ta'adda 1,427 tun farkon wannan shekara, 72 daga cikinsu a makon da ya gabata, a arewacin Iraƙi da Siriya," in ji Akturk.

Daga cikin wadannan, an kashe 681 a Iraƙi da 746 a arewacin Siriya. Ya kuma jaddada ci gaba da yin hadin gwiwa da tattaunawa da ake yi da da kasar Iraƙi wajen yaƙi da ta'addanci.

Har ila yau, Akturk ya yi karin haske kan matakan da Turkiyya ta dauka na ba da kariya ga iyakokin kasar, inda ya ce a cikin makon da ya gabata, an kama mutum 340 da suka hada da 'yan ta'adda hudu da suke yunƙurin ƙetarawa kan iyaka ba bisa ƙa'ida ba.

Tun daga farkon wannan shekara an hana mutum 65,225 wucewa ba bisa ƙa'ida ba.

Iraƙi, F-16, da Siriya

Dangane da ayyukan yanki kuwa, Akturk ya jaddada cewa, Turkiyya na ci gaba da yin hadin gwiwa da tattaunawa da maƙwabciyarta Iraki wajen yaki da ta'addanci.

Majiyoyin ma'aikatar sun kara tabbatar da aiki tare da hukumomin Iraƙi don kafa cibiyar hada-hadar kudade.

“Ana samun nasarar gudanar da ayyukanmu na yaki da ta’addanci a fagen. Muna gudanar da ayyuka masu inganci da haɗin kai tare da hukumomin Iraƙi da hukumomin yankin.

"Har ila yau ana ci gaba da gudanar da ayyukan fasaha da ke da nasaba da kafa cibiyar gudanar da ayyukan hadin gwiwa ba tare da wata matsala ba,” kamar yadda suka shaida wa kafafen yada labarai na cikin gida.

Dangane da sayen jiragen yaƙi samfurin F-16 daga Amurka, sun bayyana cewa an sanya hannu kan kwangiloli, tare da ci gaba da aiki dalla-dalla.

Majiyar ta kara da cewa, "Wannan tsari ne mai dimbin yawa. Dangane da alakar da ke tsakaninta da kasar Siriya, ma'aikatar ta jaddada aniyar Turkiyya ta kawar da barazanar ta'addanci, da kare iyakokinta a karkashin ingantacciyar ka'ida, da kuma tabbatar da samun dauwamammen kwanciyar hankali a yankin Siriya.

TRT World