Erdogan ya ce Turkiyya na kafa shingaye tsakaninta da ƙungiyoyin 'yan ta'adda da ke neman shigar da ita cikin rikici. . / Photo: AA

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce, "Ta hanyar kafa hanyar tsaro a kan iyakokinta na kudanci, Turkiyya na samun nasarar katange kanta daga yaɗuwar ayyukan ta'addanci da tashin hankali."

A wani gangamin zaɓe da aka gudanar a Lardin Sirnak na kasar Turkiyya gabanin zaben kananan hukumomin da za a yi a ranar 31 ga watan Maris, Erdogan ya ce: "Muna hana yaduwar wutar da ke kewaye da mu gaba ɗaya zuwa Turkiyya ta hanyar kafa wata hanyar tsaro a kan iyakokinmu na kudanci."

Ya kuma jaddada cewa, Turkiyya na kafa shingaye tsakaninta da ƙungiyoyin 'yan ta'adda da ke neman shigar da ita cikin rikici.

Shugaba Erdogan ya yi tsokaci game da nisantar da ‘yan mulkin mallaka da ‘yan barandansu, yana mai nuni da ƙungiyar ta’addanci ta PKK/YPG, da kuma ƙasashen da Turkiyya ke zargi da tallafa wa waɗannan ƙungiyoyin ta’addanci a kan iyakokinta da Iraƙi da Siriya.

A cikin sama da shekaru 35 na ta'addancin da ta yi kan Turkiyya, ƙungiyar ta'adda ta PKK - wacce Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai suka sanya a jerin ƙungiyoyin 'yan ta'adda - ta ɗauki alhakin mutuwar sama da mutum 40,000 da suka haɗa da mata, yara da jarirai. YPG shi ne reshen ƙungiyar na Siriya.

TRT World