Turkiyya ta fitar da kayayyakin miliyan 2 ta hanyar kasuwancin intanet a watan Mayu

Turkiyya ta fitar da kayayyakin miliyan 2 ta hanyar kasuwancin intanet a watan Mayu

Kayayyakin da aka yi a Turkiyya a manhajar kasuwancin intanet ta Trendyol su ne suka fi farin jini a
An sayar da kayayyakin da ke ɗauke da tambarin "Made in Türkiye" a biranen Baku da Riyadh da Jeddah da Dubai da kuma Bucharest. / Hoto: AA      

Kamfanonin Turkiyya sun sayar da kayayyaki na kusan miliyan biyu a watan Mayu waɗanda aka fitar da su ƙasashen waje ta manhajar kasuwanci ta Trendyol.

Tufafi da kuma kayayyakin gida su ne kan gaba a cikin samfuran kayayyakin da aka fi siya, kamar yadda Trendyol ta bayyana a ranar Alhamis.

Ƙasashen da aka fi kai kayayyakin da Turkiyya ke kasuwancinsu ta katafariyar manhajar sune Azerbaijan da Yankin Ƙasashen Tekun Fasha da Tsakiya da Gabashin Turai da Jamus da kuma Austria.

Kayayyakin da aka fi buƙata baya ga tufafi sun haɗa da kwanuka da kwantenar aijiya da katifu a cewar bayanan Trendyol.

An sayar da kayayyakin da ke ɗauke da tambarin "Made in Türkiye" a biranen Baku da Riyadh da Jeddah da Dubai da kuma Bucharest.

Trendyol dai na ci gaba da ƙarfafa wa abokan cinikayyarsa ta hanyar samar da tsarin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje cikin sauki, inda 'ya zuwa yanzu kafar ta siyar da samfuran kayayyaki miliyan ɗaya zuwa ƙasar Azerbaijan a yayin wani gangamin fitar da kayayyaki da aka yi take "Mega May" zuwa ƙasar.

Katafariyar manhajar ta cinikayya ta intanet tana gabatar da kayayyakin da ake yi a Turkiyya da waɗanda ak yi don cikin gida zuwa kasuwannin duniya, inda ta taimaka wa fiye da 'yan kasuwa 90,000 na gida suka sauya zuwa sayar da kayayyakinsu ta intanet a bara, ta hanyar wasu dabarunta, inda aka fitar da kayakkin da suka kai na dala miliyan 650 a shekarar 2023.

Trendyol ya sami lambar yabo daga Majalisar Masu fitar da kayayyaki ta Türkiye (TIM) saboda gudummawar da ta bayar wajen kasuwancin fitar da kayayyaki ta intanet.

TRT World