Sweden ta jaddada cewa ba za ta goyi bayan kungiyoyin ta’addanci na YPG/PYD da FETO ba. /Hoto:AA

Turkiyya ta amince ta tura wa majalisar dokokin kasar bukatar Sweden ta shiga kungiyar NATO, kamar yadda sakataren NATO Jens Stoltenberg ya bayyana a jajiberin taron na kungiyar wanda za a yi a Vilnius.

“Ina farin cikin sanar da cewa... Shugaba Erdogan ya amince ya tura bukatar Sweden ta shiga NATO ga babban zauren majalisa nan ba da jimawa ba, tare da aiki da majalisar domin amincewa,” kamar yadda Stoltenberg ya bayyana a yayin taron manema labarai a ranar Litinin.

Stoltenberg ya ki bayar da ranar da Majalisar Turkiyya za ta amince da batun.

Amincewar Turkiyya na zuwa ne bayan Stockholm ta amince ta kulla yarjejeniyar tsaro da Ankara, in ji Stoltenberg.

Haka kuma Sweden din za ta bayar da goyon baya ga shirin Turkiyya na shiga Tarayyar Turai, kamar yadda ya kara da cewa.

Ya bayyana cewa NATO a karon farko ta samar da mukamin babban jami’in da ke yaki da ta’ddanci.

Sweden ta jaddada cewa ba za ta goyi bayan kungiyoyin ta’addanci na YPG/PYD da FETO ba, a wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar bayan tattaunawa tsakanin Turkiyya da Sweden da kuma shugaban NATO.

Kawayen Turkiyya sun jinjina wa matakin kasar

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi maraba da matakin Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan na goyon bayan Sweden domin shiga NATO.

“A shirye nake na soma aiki da Shugaba Erdogan da Turkiyya kan inganta tsaro a yankin Turai,” kamar yadda Biden ya bayyana a wata sanarwa inda ya kara da cewa:

“Ina sa ran maraba da Firaiminista Kristersson da Sweden a matsayin kawarmu ta 32 a NATO.”

Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock, ita ma ta yi maraba da wannan matakin inda ta ce: “Turkiyya ta bude hanyar Sweden ta shiga kungiyar NATO,” kamar yadda Baerbock ta rubuta a Twitter.

Firaiministan Birtaniya Sunak ya kira matakin na Turkiyya “lokaci na tarihi ga NATO”.

Finland da Sweden duk sun nemi shiga NATO bayan soma yakin Russia da Ukraine a Fabrairun 2022. Turkiyya ta amince da Finland ta shiga NATO.

Dole ne Sweden ta samu amincewar duka mambobin kungiyar, ciki har da Turkiyya wadda take cikin kungiyar sama da shekara 70, kafin ta shiga NATO. Turkiyya ce ta biyu a yawan kasashen da ke da sojoji a kungiyar.

TRT Afrika da abokan hulda