Turkiyya ta aika jirgin ruwanta na 14 da ke ɗauke da kayayyakin jinƙai zuwa Gaza domin biyan buƙatun Falasɗinawa da suka rasa matsugunansu, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar, Ali Yerlikaya.
''Mun ƙaddamar da shirinmu na #ShipOf Goodness don samun damar yi wa 'yan'uwanmu maza da mata waɗanda suka jikkata magani da kuma biyan buƙatunsu na wucin-gadi," kamar yadda Yerlikaya ya bayyana a ranar Talata a shafinsa na X.
Jirgin na ɗauke da tantuna 10,460 da barguna 14,350, da banɗaki na wucin-gadi 20, da janareta 300, da sauransu, in ji shi.
Ministan ya jaddada ƙudurin Ankara na taimaka wa mabuƙata, yana mai cewa,"kamar yadda aka saba yi a baya, a yanzu ma za mu ci gaba da tallafa wa waɗanda ake zalunta tare da miƙa taimakon al'ummarmu ga musu buƙata.''
Tallafin na jirgin dai ya nuna irin goyon bayan da Turkiyya ke bai wa Falasɗinawa da kuma ƙoƙarinta na ganin an shawo kan matsalar jinƙai a Gaza, bayan Isra'ila ta lalata yankin ta hanyar amfani da jiragen sama mara makuƙa da manyan makamai kafin ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙungiyar Hamas bayan shafe sama da watanni 15 tana kai hare-hare.
Tun daga ranar 19 ga watan Janairu ne yarjejeniyar tsagaita wutar ta soma aiki, matakin da ya kai ga datakar da yakin kisan kare dangi na Isra'ila wanda ya salwantar da rayukan Falasɗinawa sama da 47,300 waɗanda galibinsu mata da ƙananan yara ne tare da jikkata sama da mutum 111,400 tun daga daga ranar 7 ga watan Oktoba, 2023.
Yakin ya kuma yi sanadin batan mutane sama da 11,000 tare da haifar da rikicin jinƙai da wanda ya yi sanadin salwantar da rayukan tsofaffi da yara da dama, lamarin da ya haifar da daya daga cikin bala'o'in jinƙai mafi muni a duniya.
A watan Nuwamban bara ne kotun hukunta manyan laifuka duniya (ICC) ta bayar da sammacin kama Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaron ƙasar Yoav Gallant bisa laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a Gaza.
Kazalika, Isra'ila na fuskantar tuhuma kan kisan kiyashi a kotun kasa da kasa ta ICJ kan yakin da ta ke yi da yankin.