Turkiyya ta fara shiga tsakani a tattaunawar da ake yi tsakanin Somaliya da Habasha, wadda dangantakarsu ta yi tsami bayan yarjejeniyar tashar ruwa da Habasha ta rattabawa hannu da yankin Somaliland a farkon wannan shekara.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta faɗa a ranar Litinin cewa, babban jami'in diplomasiyyar ƙasar Hakan Fidan ya karɓi baƙuncin takwarorinsa na Habasha da Somaliya a Ankara, tana ƙarawa da cewa jami'an uku sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar haɗin gwiwa bayan wata tattaunawar "gaskiya da gaskiya da fahimtar juna da fatan samun mafita" kan bambance-bambancensu.
Ministocin na Somaliya da Habasha sun tattauna kan hanyoyin da za su bi su warware bambance-bambancensu "ta hanyar da suka amince da ita" tare da amince wa su sake wata tattaunawar a Ankara ranar 2 ga Satumba, a cewar sanarwar.
"Ministocin na Somaliya da Habasha sun jaddada ƙudirinsu na warware matsalar cikin ruwan sanyi," a cewar sanarwar.
Wani mai magana da yawun yankin Somaliland, wanda yake ta ƙoƙarin a amince da shi a duniya duk da mulkin gashin kai da kuma samun yanayi na kwanciyar hankali tun bayan ayyana 'yancin kai a 1991, ya ce ba a saka yankin cikin tattaunawar ba.
Yunƙurin Turkiyya a Afirka
Turkiyya ta zama babbar ƙawar gwamnatin Somaliya tun bayan ziyarar farko da Shugaba Recep Tayyip Erdoga ya kai Mogadishu a 2011, da horar da jami'an tsaronta, da aike mata da tallafin kayan ci gaban ƙasa.
Ƙasashen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro a watan Fabrairu, wacce a ƙarƙashinta Ankara za ta samar da tallafin tsaron teku ga Somaliya don taimaka wa ƙasar ta Afirka kare tekunta.
Turkiyya ta gina makarantu da asibitoci da samar da kayayyakin ci gaba ta kuma samar da tallafin guraben karatu ga 'yan Somaliya su yi karatu a Turkiyya, inda ita kuma ta samu wajen zama a Afirka da kuma muhimman hanyoyin jirage ruwa na duniya.
Majiyoyin diplomasiyyar Turkiyya sun ce Ankara ta fara shiga tsakani ne bayan Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya ziyarci Erdoga a Ankara a watan Mayu sannan ya gabatar da wata wasiƙa yana neman Turkiyya ta sasanta Somaliya da Habasha.
Saɓani da rikici
An fara samun saɓani tsakanin ƙasashen na Afrika biyu ne tun bayan da da Habasha ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da yankin Somaliland da ya ɓalle a watan Janairu, abin da Somaliya ta bayyana a matsatin kutse cikin 'yancin cin gashin kanta.
Yarjejeniyar za ta bai wa Habasha wacce ba ta da gaɓar ruwa damar yin amfani da teken Somaliland, ita kuma Habasha za ta rama wa yankin ta hanyar amince wa da shi a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta
Ƙasashen biyu suna da tarihin rikici da saɓani da yaƙi da juna a ƙarni na 20.
Har zuwa 1960 yankin Somaliland yana ƙarƙashin mulkin mallakar Birtaniya. Ya shafe kwanaki biyar a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, kafin ya haɗe da Somaliya don raɗin kansa.
A ɗaya ɓangaren kuma, an kange Habasha daga gaɓar teku bayan Eritrea ta ɓalle ta ayyana 'yancin gashin kai a 1993, bayan shafe shekaru 30 ana yaƙi.