Joseph Borrell ya yi wannan tsokaci a taron manema labarai, ind ayake bayyana tsarin fadada manufofi na 2024. / Photo: AFP

Shuguban tsara manufofin Tarayyar Turai a ƙasashen waje ya ce "Turkiyya ƙasa ce mai neman takarar shiga Tarayyar, wadda muhimmancinta a yankin ya ƙaru sosai a hali da yanayin da ake ciki."

Joseph Borrell ya yi wannan tsokaci a taron manema labarai, inda yake bayyana tsarin faɗaɗa manufofi na 2024, wanda ya ƙunshi duba ga ƙasashen da ke neman shiga Tarayyar Turai irin su Turkiyya, Serbia, Albania, Montenegro, Macedonia ta Arewa, Bosnia da Herzegovina, Kosovo, Ukraine da Maldova.

Da yake bayyana yadda za a yi "aiki da yawa don kawar da tsamar da ke tsakanin alakar Tarayyar Turai da Turkiyya," inda Borrell ya ce: "Da fari, abubuwa na da wahala ba kamar yau ba. Mun sake kusantar juna a ɓangarorin da muke da manufofi a akai baki ɗaya."

Da yake bayyana muhimmancin Turkiyya ga ƙawancen, Borrell ya ce "Turkiyya, tana da muhimmanci. Tana da muhimmanci ne saboda halin da ake ciki a yankin babban ƙalubale ne, kuma babban ƙalubalen shi ne yadda lamarin ya daɗe."

"Kuma 'yan ƙasashen Turai na sa ran Tarayyar Turai ta samu damar tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai da maƙotanmu, da ke kewaye da mu," in ji shi.

Borrell ya kuma ambaci wani ci gaba da aka samu a bangarori irin su na kasuwanci, bincike da kirkire-kirkire, da manufofin tattalin arziki da kudi, yana mai cewa an yaba da kokarin Turkiyya a wadannan bangarori.

"Rahoton Turkiyya" da ke cikin Tsarin Faɗaɗa Manufofi na 2024 ya bayyana cewa akwai ci gaban haɗin kai, alaƙar cude-ni-in-cude-ka da Tarayyar Turai, yana mai haskaka rawar da kasar ke takawa a matsayin jarumar manufofin ƙasashen waje da 'yancin samar da dabarun cim ma manufofi.

Kawa mai muhimmanci, abokiyar aiki a NATO

Kwamishinan Tarayyar Turai Kan Maƙota da Fadada Manufofi, Oliver Varhelyi, ya sanar a yayin ziyara a Ankara a watan Satumba cewa Tarayyar Turai na farfaɗowa da haɓaka alakƙarta da Turkiyya.

Ya ce ana kallon Turkiyya a matsayin 'yar takarar shigaba Tarayyar, abokiya mai muhimmanci, kuma babbar ƙawa a NATO, yana mai tsokaci da cewa dukkan ɓangarorin biyu sun yanke shawarar warware batutuwa da dama game da Ƙungiyar Fito.

Ya kuma jaddada fatan ci gaba da tattaunawar shugabannin ɓangarorin, sabunta ayyukan Bankin ZUba Jari na Turai, da sake duba ga tsarin sabunta yarjejeniyar Shiga da Fitar da Kayayyaki tsakanin Tarayyar Turai da Turkiyya,.

A shekarar 1987 ne Turkiyya ta nemi shiga Tarayyar Turai, kuma tun 1999 ta zama 'yar takarar neman shigar. A watan Oktoban 2005 ne aka fara tattaunawar ganin ta shiga Tarayyar, amma bayan 2007 sai aka dakata saboda batun tsibirin Cyprus d akuma yadda kasashe da dama suka nuna adawa da shigar Turkiyya kawancen.

Dabarun Turkiyya don cimma manufofinta

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci Rasha a makon da ya gabata don ganawa da shugabannin BRICS, a yayin da Ankara ke neman zama mambar ƙawancen.

Bayan taron majalisar ministoci a Ankara a ranar Litinin, Erdogan ya yi ƙarin haske cewa ƙawancen da Turkiyya ke ƙullawa da ƙasashen BRICS ba yana nufin maye gurbin alaƙarta da ƙasashen duniya ba ne.

Ya yi ƙarin haske da cewar Turkiyya ba wai tana sauya akalarta ba ne amma tana aiki don samun gurbin zaman da ya kamace ta a lokacin da duniya ke sauyawa.

Da yake sake jaddada daidaitattun manufofin kasashen waje, Erdogan ya yi tsokaci da cewa ""Muna neman haɗin-kai da duk waɗanda manufofin Turkiyya suka shafa."

TRT World