Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da firaministan Malaysia Anwar Ibrahim sun sanar da shirin ninka yawan kasuwancin da ke tsakanin kasashensu daga dala biliyan 5 zuwa dala biliyan 10.
Bayan hadin gwiwar tattalin arziki, da rattaba hannu kan yarjejeniyoyin 11 a Malaysia, shugabannin sun kuma tunkari matsalolin da suka shafi duniya, tare da mai da hankali sosai kan matsalar jinƙai a Gaza.
Da yake jawabi a wajen taron a ranar Talata, Shugaba Erdogan ya yi kira da a gaggauta kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yi a yankunan Falasdinawa, yana mai jaddada bukatar daukar mataki.
Erdogan ya ce "Dole ne Isra'ila ta kawo karshen mamayar da take yi wa yankunan Falasdinawa, ta kuma biya diyya ga ɓarnar da ta yi."
Da yake nanata matsayar Turkiyya da ta dade a kan batun samar da kasashe biyu, ya jaddada muhimmancin kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta bisa kan iyakokin shekarar 1967, tare da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta.
Goyon baya daga ƙasashen duniya
Ya ce, "Yana da matukar muhimmanci a kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, da hadin kan yankuna, tare da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta," in ji shi.
Dangane da taimakon jinƙai ga Gaza, Erdogan ya jaddada muhimmancin hadin kan kasa da kasa, musamman a tsakanin kasashen ASEAN, wajen tinkarar rikicin.
"Idan dukkan mambobin ASEAN suka hada hannu, na yi imanin za mu iya shawo kan wannan kalubale," in ji shi.
Firayim Minista Anwar Ibrahim ya yaba wa jagorancin Erdogan, yana mai bayyana shi a matsayin mai kare adalci da kare hakkin bil'adama.
Anwar ya ce "Muna matukar farin ciki da karbar bakuncin shugaban da ya tsaya a matsayin mai kare adalci da kare hakkin bil'adama ga duniyar Musulmai."
Ya kara da cewa, "Idan ana batun Gaza, Turkiyya ta dauki nauyin jagoranci, babu wata kasa da ta kai Turkiyya wajen bayar da agaji."