A martanin kan kalama da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ministan harkokin wajen kasar Eli Cohen suka yi a baya-bayan kan shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya yi watsi da yunƙurinsu na karkatar da hankalin duniya daga abin da ya kira "laifukan yaƙin da suke aikatawa a kan fararen hula.
"Ba mu yi mamakin kokarin Firaiministan Isra'ila da Ministan Harkokin Wajen Isra'ila na janye hankalin duniya daga laifukan yaki da suke aikatawa kan fararen hula ba," in ji Altun a ranar Alhamis.
Ya ci gaba da bayyana irin yadda gwamnatin Isra'ila ke yada labaran ƙarya kan ayyukan da suke yi a Gaza, yana mai cewa Shugaba Erdoğan ya jajirce wajen fadin gaskiya.
"Shugabanmu Erdogan bai taba jin tsoron fadin gaskiya ba kuma zai ci gaba da yin haka,” in ji Altun.
Da yake jaddada abubuwan da suka faru a Gaza a fili a cikin watan da ya gabata, ya jaddada cewa, babu wani abu da zai iya ruguza hakikanin gaskiyar da duniya ta shaida.
'Netanyahu yana lalata zaman lafiya'
Da yake jawabi kai tsaye ga firaministan Isra'ila Netanyahu, Altun ya ayyana shi a matsayin wanda ya shafe shekaru da dama yana gurgunta fatan zaman lafiya.
"A matsayinsa na dan siyasa wanda ya gina aikinsa wajen ruguza duk wata dama ta samar da zaman lafiya a tsawon shekaru da dama, a fili yake cewa Netanyahu ba zai iya jure sauraron gaskiya a kan yakin da yake yi na kai hari kan fararen hula Falasdinawa ba," in ji wakilin na Turkiyya.
Da yake zargin Netanyahu da wasu masu tsattsauran ra'ayi na gwamnatin Tel Aviv da hannu dumu-dumu a mamaya, da kisan kare-dangi, da laifukan yaki, Daraktan Sadarwar ya ce ba su da sha'awar samar da zaman lafiya a yankin.
"Ba su da wata sha'awar samar da zaman lafiya a wannan yanki kuma za su ci gaba da yin yaki a duk wata dama da suka samu," in ji shi.
"Dole ne duniya ta dauki mataki yanzu don ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa duk da cewa 'yan siyasar Isra'ila sun dage wajen ta'azzara tashin hankali na dindindin," in ji Altun.
Ya yi kira da a hada kan duniya wajen neman zaman lafiya da adalci, yana mai yin Allah wadai da laifukan da 'yan siyasar Isra'ila suka aikata kan fararen hula Falasdinawa.
"Dole ne mu hana su mummunan tunaninsu ta hanyar hada kai don samar da zaman lafiya da adalci," in ji Daraktan Sadarwa na Turkiyya.
Ya yi watsi da sukar da aka yi wa shugabancin Turkiyya a matsayin ƙarya da ɓatanci, yana mai cewa Isra'ila ta riga ta sha kashi a kotun sauraron ra'ayin jama'a.
"Duk da tsare-tsare na farfaganda da yada labaran ƙarya da Isra'ila ke yi, za mu ci gaba da yin duk abin da za mu iya don samar da zaman lafiya. Turkiyya ba za ta taɓa yin watsi da Falasdinu ba.
Tun daga Oktoba 7 2023, bayan da Isra'ila ta fara kai hare-hare a Gaza bayan harin Hamas, aƙalla Falasdinawa 11,500 ne suka mutu, ciki har da mata da yara kusan 8,000, yayin da wasu fiye da 30,000 suka jikkata, a cewar sabbin alkaluman hukumomin Falasdinu.
Wani labarin mai alaƙa: Isra'ila ta nuna zallar mugunta da kama-karya da wariya: Fahrettin Altun