Shugaban Turkiya Recep Tayyip ya jaddada cewa kasarsa ba za ta zura ido tana gani ana cin zarafi da kuma yin barazana ga matsayin Masallacin Kudu, na uku mafi tsarki ba.
Ya bayyana haka ne ranar Asabar yayin kiran wayar da ya yi wa takwaransa na Isra’ila Isaac Herzog inda suka tattauna game da hare-haren baya-bayan nan da dakarun Isra’ila suke kai wa Masallacin Kudus.
Ma’aikatar watsa labarai ta Turkiyya ta ambato Shugaba Erdogan yana cewa hare-haren wulakanci ne ba kawai ga Musulmai ba, har ma ga dukkan ‘yan adam.
Erdogan ya nanata bukatar kare Masallacin Kudus daga dukkan barazana, yana mai jaddada irin muhimmancinsa a duniya.
Abin da ya sa Masallacin Kudus ke da matukar muhimmanci ga Musulmai
Ya kara da cewa bai kamata a bari a cigaba da tayar da jijiyoyin wuya a yankin Gaza da Lebanon ba.
Ankara ta shirya taka muhimmiyar rawa
Shugaban na Turkiyya ya bayyana bukatar hana aukuwar irin wadannan hare-hare nan gaba, musamman a watan Ramadana mai albarka.
Erdogan ya kara da cewa a shirye kasarsa take ta shiga tsakani domin gano asalin matsalar da kuma shawo kanta ta hanyar yin adalci da samo mafita ta dindindin.
Rikici ya watsu ne zuwa yankunan Falasdinawa bayan dakarun Isra'ila sun kai hari Masallacin Kudus inda suka tursasa wa masallata fita daga cikinsa ranar Talata da Larabar da suka wuce.
Hare-haren da dakarun Isra'ila suka kai masallacin sun jawo zazzafan martani inda aka rika harba wa kasar makaman roka daga yankin Gaza da Lebanon, yayin da ita kuma ta rika kai hari ta sama.
Falasdinawa suna zargin Isra'ila da kokarin mamaye Gabashin Kudus, inda Masallacin Kudus yake, sannan ta kawar da dukkan shaidun da ke nuna alakarsa da Larabawa da Musulmai.